Kannywood

Yan Sanda Sun Gurfanar Da Jaruma Amal Umar A Gaban Kotu

‘Yan Sanda Sun Gurfanar Da Jarumar Kannywood Amal Umar A Gaban Kotu

Amal Umar

Rundunar ‘yan sanda shiyya ta ɗaya Zone One, dake jihar Kano, ƙarƙashin AIG Umar Mamman Sanda, sun gurfanar da guda daga cikin ‘yan masa’antar shirye fina-finan Hausa ta Kannywood, mai suna Amal Umar, a gaban kotun majistiri mai lamba 24, dake zamanta a unguwar Gyadi-Gyadi.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sandan shiyya ta ɗaya CSP Bashir Muhammad ya fitar, aka aikawa manema labarai.

An dai gurfanar da Amal Umar ne a gaban kotun bisa zargin ta da yunƙurin bada cin hancin Naira dubu ɗari biyu da hamsin (250,000), ga ɗan sandan da ke bincike a kan wani laifi da ake zargin da hannun ta wajan aikata wa.

Yanzun Haka Dai Jaruman KannyWood Sun Fara Nuna Rashin Jin Dadinsu Game Da Kama Abokiyar Aikin Nasu, Inda Su Fara Wallafa #JusticesforAmalUmar Wato Suna Neman Aima Amal Umar Adalci.

 

Back to top button
error: Content is protected !!