Labarai

‘Yan Sanda Sun Gayyaci Sarkin Kano Zuwa Abuja Saboda Rikicin Ranar Sallah

Sarkin Kano sunusi
Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya ta gayyaci Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II zuwa Abuja a binciken da take yi kan wata hatsaniya da aka yi a Kano a ranar Ƙaramar Sallah.

An yi hatsaniyar ne a ranar 30 ga Maris, 2025, inda wasu magoya bayan Sarkin suka yi arangama da masu adawa da shi har wani ɗan bijilanti ya rasa ran sa.

Sakamakon haka, ‘yan sanda a Kano suka kama wani matashi ɗan shekara 20 mai suna Usman Sagiru, daga unguwar Sharifai, ana zargin sa.

Daga bisani suka gayyaci Shamakin Kano Alhaji Wada Isyaku, suka yi masa tambayoyi kan lamarin.

Yanzu kuma an ce Sarki da kan sa ya je Abuja ana neman sa.

A takardar gayyatar da aka rubuta ranar 4 ga Afrilu, 2025, ɗauke da sa hannun Kwamishinan Aikace-aikace CP Olajide Rufus Ibitoye, an ce ana so Sarki Sanusi ya bayyana a sashen C.I D. na hedikwatar rundunar a ranar Talata mai zuwa, 8 ga Afrilu, da karfe 10 na safe.

An shaida masa cewa Sufeto Janar na ‘Yan Sanda ne ya ba da umurnin a gayyace shi ɗin saboda hatsaniyar da aka yi a masarautar sa a ranar Sallah.

Takardar ta ce: ”I have the directives of the Inspector General of police, through the Deputy Inspector General of Police, Force Intelligence Department (FID) to invite you for an investigative meeting with regards to an incident that occurred during the Sallah celebration within your domain.

”In view of the above, you are hereby invited to Force Intelligence Department, opposite Police force headquarters Area 11, Abuja by 1000hrs of Tuesday 8th of April, 2025.”Your availability is highly sought for a purposeful investigation. Accept the warm regards of the Deputy Inspector General of Police, please.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!