Labarai
Yan Sanda Ne Suka Dakeni, Kuma Gwamna Uba Sani Nake Zargin Ya Turosu
Yan Sanda Ne Suka Dakeni, Kuma Gwamna Uba Sani Nake Zargin Ya Turosu. – Dan Balki Kwamanda
Biyo bayan wani faifan bidiyo daya karade shafukansa sada zamunta wanda ke nuna yadda wasu da ba’asan ko suwaye ba suke dukan fitaccen dan siyasar nan Abdulmajeed Dan Bilki Kwamanda.
Yanzu haka dai Dan bilki ya wallafa wani faifan bidiyon dake bayanin abinda ya faru a wancan bidiyo.
Dan Bilki yace “jami’an yan sanda ne suka dakeshi bayan sun kaishi bakin kogi tare da yi masa barazanar zasu kashehi, kuma ba kowa yace zargi ya turosu ba sai Gwamnan Jahar Kanduna Uba Sani”.
Daga Ibrahim Aminu Makama