E News
Yan Nageriya Sun Girgiza Bayan Kotu Ta Wanke Ganduje
‘Yan Nageriya sun girgiza bayan Jin labarin kotu ta wanke Ganduje daga Hukuncin rashawa.
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta yanke hukuncin cewa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ba ta da hurumin binciken tsohon Gwamna kuma Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje kan wani faifan bidiyo na cin hancin dala.
A karar da Ganduje ya shigar gabanta, ta bayar da umarnin hana binciken hukumar kan bidiyon. Ganduje dai ya yi zargin cewa hukumar ba ta da hurumi, kuma kotun ta amince, inda ta ce laifin da ake zargin Ganduje na Gwamnatin tarayya ne wanda kuma ya kamata hukumomi irin su hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ne za su binciki lamarin.