‘Yan KannyWood Za Suyi Wa Ali Nuhu Dinar Taya Murna
‘YAN masana’antar shirya finafinai ta Kannywood a yau Litinin za su shirya wa sabon Darakta-Janar na Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (NFC) kuma jarumi Ali Nuhu gagarumar dina domin taya shi murnar samun muƙamin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa shi
Kamar yadda shugabar kwamitin tsara-tsare na bikin, tsohuwar jarumar Kannywood, Hajiya Hindatu Bashir, ta bayyana, za a gudanar da biki ne a ɗakin taro na otal ɗin ‘The Afficent Grand’ da ke lamba 13, Titin Magaji Rumfa, Kano.
Haka kuma an yi tsari da ƙa’idojin gudanar da bikin kamar haka:
* Sai wanda ke da katin shaida na musamman kaɗai ne zai shiga ɗakin taro.
* Akwai katin manyan baƙi na musamman (VIP), akwai kuma na gama-gari domin girmama baƙi da nuna ɗa’ar da wakiltar al’adun mu.”
Sanarwar ta ce: “Ya zama dole kowa ya mutunta katin shigar da aka ba shi domin da shi ne masu tarar baƙi (ushers) za su nuna maka inda za ka zauna,” inji mashirya bikin.
Hindatu Bashir ta ci gaba da cewa, “Taro ne na mutum 1,000 kawai domin ɗakin taron iya mutanen da zai iya ɗauka kenan, don haka ba kowa ne zai samu katin shiga ba. Idan ba ka samu ba wasu za su wakilce ka, sai ka bada haɗin kai don girmama juna, domin idan ka je babu kati, jami’an tsaro ba za su bar ka ka shiga ba.
“Sannan, sai kati mai ɗauke da ‘stamp’ da ‘signature’ ne kaɗai za a yarda ya shiga wannan taro. Idan katin da aka ba ka babu ɗaya daga cikin wannan ka nemi Mudassir Ƙasim cikin gaggawa.
“Mun tsara kowace ƙungiya da sashe-sashe, za a ba wa wakilan su katin shiga domin su raba musu, don haka ka nemi jagoran ƙungiyar ku domin karɓar katin ka iya wanda ya samu.”
Bugu da ƙari, shugabar ta ce, “A cikin ɗakin taron, mutane dubu ɗaya ne aka gayyata, don haka kowa ya na da wurin zama isasshe, kuma za a kawo maka abinci har wurin.
“Ba a yarda da tashi ko zirga-zirga daga wannan waje zuwa can ba, matuƙar kai ba ‘official’ ko ‘usher’ ko ‘press’ ba ne.
“Akwai ‘officials’ da ‘ushers’ a wannan taro duk abin da ka ke buƙata ka neme su za su taimaka.
“‘Ushers’ za su tare ka su ba ka wurin zama, don haka ka girmama su kamar yadda ka ke so a girmama ka, domin su ma gudunmawar su ce su ka bayar don taro ya yi kyau, kuma a mutunta sana’ar da ka ke taƙama da ita.
“Haka kuma, an tsara wurin rawa daban, wurin jawabi daban. Ba a yarda wani ko wata su je wurin da aka tanada don jawabi su yi rawa ba.
“Ba a yarda kowa ya liƙa wa MD kuɗi ba, doka ce ta Nijeriya. Don Haka babu liƙi.
“Mun kama waje ne a keɓance don mu yi murna. Don haka cin amana ne tozarta ɗan’adam ne ka ɗauke shi ya na rawa, kuma ka saka a ‘social media’, duk wanda ya yi haka doka za ta iya aiki a kan shi.
“Ba a yarda da ɗauke-ɗauken hoton abin da ke gudana a ‘stage’ ba matuƙar ba masu hoton da aka tanada ba.
“Akwai jami’an tsaro wadatattu da aka tanada don tsaron lafiyar ka da kare mutuncin ka, don haka duk wanda ya nemi cin zarafin wani ko wata za a fitar da shi daga ɗakin taro kai-tsaye.
“Mu na matuƙar godiya ga ‘yan’uwa da za mu haɗu a wannan wurin taro don taya ɗan’uwan mu da ya samu muƙami murna.
A ranar Juma’a, 12 ga Janairu, 2024 ne dai aka bayyana naɗin Ali Nuhu a matsayin shugaban na NFC wadda ke ƙarƙashin Ma’aikatar Fasaha Da Al’adu Da ta Tarayya.