‘Yan KannyWood Sun Nuna Wa HuKumar Hisbah Yatsa
‘Yan KannyWood Sun Nuna Wa HuKumar Hisbah Na Jihar Kano Yatsa, Kan Gayyatar Data Musu.

Bisa ga dukkan alamu dai za a kai ruwa rana tsakanin hukumar Hisbah ta Jihar Kano da ‘yan Kannywood a game da matakin da hukumar ta ce ta na bi na kawo gyara da kuma tsari a cikin zamantakewar jama’ar jihar.
A jiya Juma’a ne mataimakin babban Kwamandan hukumar, Dakta Mujahid Aminudden, ya bada sanarwar cewa hukumar ta na gayyatar dukkan ‘yan fim zuwa ofishin ta a ranar Litinin mai zuwa domin ganawa da su.
Ya ce: “A baya mun gana da ƙannen ku ‘yan TikTok, a yanzu kuma mu na kira da ku ma ku zo a zauna da ku kuma a game da yadda ku ke gudanar da harkar ku.”
To sai dai tun daga fitowar sanarwar aka fara samun turjiya daga wajen ‘yan fim ɗin.
Shugaban ƙungiyar jarumai, Alhassan Kwalle, ya ce sam ba su ji daɗin irin wannan gayyatar da hukumar ta yi masu ta kafafen yaɗa labarai ba, domin kuwa sun wuce a yi masu gayyata irin wadda aka yi wa ‘yan TikTok, ya ce yin hakan bai cancanta ba.
Ya ce a maimakon haka, kamata ya yi a rubuta masu takardar gayyata kamar yadda su ka saba yi da sauran hukumomi har ma da Hisbah ɗin a lokuta daban-daban. Kamar yadda su ma idan su na son zama da wata hukuma su kan rubuta mata takarda kuma a ba su lokaci a saurare su.
Kwalle ya ce a matsayin Kannywood na babbar masana’anta mai tsari na shugabanci ta wuce a yi mata irin wannan gayyata.
Shi kuwa Babban furodusa, Umar Sani Ƙofar Mazugal, wanda aka fi sani da Umar U.K., cewa ya yi: “Ni ba zan amsa kiran da hukumar ta Hisbah ta yi ba, don ina da ‘yanci, na fi ƙarfin a gayyace ni a kan titi, domin ko gwamna ne ya yi mini irin wannan gayyatar ba zan je ba.
“Ni ɗan kasuwa ne, ina gudanar da harkar kasuwanci na a cikin Kannywood, don na ji sun ce har da masu shirya fim ne, na ji abin ya shafe ni, amma sam ba zan amsa gayyatar da na ji ba kan titi ba domin babu wata takarda da aka ba ni a rubuce, don haka a kan titi na ji sanarwar.
“Kuma idan gayyatar mu gwamnati za ta yi, ai mu na da Hukumar Tace Finafinai, a ƙarƙashin ta mu ke, don me sai Hisbah ce za ta gayyace mu?
“Wannan gwamnatin tamu ce, da mu aka kafa ta, amma idan aka zo da wani tsari a cikin ta da bai yi daidai ba ba za mu yarda da shi ba. Saboda haka ni dai ba zan amsa gayyatar Hisbah da na ji a kan titi ba.”
Daga Shafin: Fimmagazine.com







