Yan Fim sun gana da sabon Kwamishinan yan Sandan Jihar Kano
Kungiyar jarumai ta kasa mai suna “Hausa Actors Guild of Nigeria” a karkashin shugabancin Alhassan Kwalle sun kai ziyara ga sabon Kwamishinan ‘ Yan sanda na Jihar Kano a shalkwatar rundunar da ke unguwar Bompai.
Ziyarar wadda aka yi ta a safiya ranar laraba 20 ga watan Nuwamba ta hada kawu nan yan fim da yawa maza da mata, a yayi zaman nasu da Kwamishinan tashin farko jagoran tafiyar nasu kuma jarumi Alhassan Kwalle ya fara bayani dangane da makasudin wannan ziyara tasu.
Alhassan Kwalle, ya bayyana cewa “Mun zo wannan waje ne domin yi maka murna da kuma sannu da zuwa wannan jiha ta mu a matsayin sabon Kwamishinan ‘Yan sanda, don haka ne mu ka zo da jama’ar mu don mu taya ka murna duk da cewa ba gaba dayan mu muka samu damar zuwa ba, amma akwai wakilci na kowanne bangare na harkar fim.
Ya cigaba da cewa, Baya ga haka kasancewar mu na masu harkokin jama’a, wannan dalilin yasa mu ka zo domin mu gabagar da kan mu yadda idan wani ya taso ya zama akwai sanin juna yadda za mu rinka taimakon juna wajen samar da zaman Lafiya, muna fatan za a dauke mu a matsayin jakadu na samar da zaman lafiya.
Ya kara da cewa ‘Baya ga haka kuma akwai wasu matsaloli da su ke damun mu a matsayin mu na ‘ yan fim, saboda a na samun bata gari da su ke fakewa da harkar su na biyan wa ta bukata ta su, a kan haka ne ma saboda da kyakkyawar alakar da ta ke tsakanin mu da hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta samar da katin shaida ga duk wasu masu harkar fim, domin magance bata garin da ke cikin harkar, wannan dalilin ya sa muke so mu sanar da Kwamishinan cewa duk wani dan fim na hakika ya na da wannan katin shaidar.
Duk kuwa wanda aka samu ba shi da wannan kati to ba dan fim ba ne kuma a hukun ta shi na yin karya, kuma muna neman alfarma don Allah kada a kalle shi a matsayin dan fim. idan kuma aka samu mai wannan katin shaidar da laifi toh shima sai a yi masa hukunci kamar yadda doka ta tanadar.
Ya kara da cewa “Baya ga haka akwai matsalar masu satar fasaha da mu ke fuskanta kuma ba za mu iya magance ta mu kadai ba sai mun hada da hukumar tsaro, don haka muna neman goyon bayan Hukumar Yan Sanda da su bamu wannan gudunmawa don gudun daukar doka a hannu. Mu na yi maka fatan alheri Allah ya sa ka gama alkin ka Lafiya”
Jawabin kwamashinan yan sandar a gare su bayan sun ga ma gabatar da kansu. ya fara da cewa “. Ina godiya da wannan ziyarar girma da Yan Fim su ka kawo mun kuma na yi alkawarin du ba bukatun ku domin daukar duk matakin da ya dace don ganin an cimma nasarar da a ka sa a gaba”.
Sannan kuma ya yi kira ga daukacin Yan Fim da su za ma masu bin doka wajen gudanar da ayyukan su, duk da cewar an san su da son zaman lafiya da kuma fadakarwa wajen a bi doka. muna fatan Hakan zai dore domin a samu cigaba a wannan jihar da ma kasa baki daya”
Daga karshe su ka mika masa tsarabar da suka je masa da ita kyauta ta musamman, in da shi kuma ya karba tare yin musu godiya da fatan alheri.