Yan Arewa Bazasu Sake Goyon Bayan Tinubu Ba
Ba yanda za’a yi ƴan Aréwa su goyi bayan Tunibu a wa’adi na biyu – Primate Ayodele
Shugaban cocin Evangelical Spiritual Chúrch, Primate Elijah Ayódele a ranar Lahadi ya gárgadi shugaban kasa Bóla Ahmed Tinubu da ya kasance yana da wata dabara game da tsariń da yake bi dón tafiyar da yankin Arewacin kasar nan saboda ba za su goyi bayan burinsa na wa’adi na biyu ba.
Primate Ayodele ya yi ikirarin cewa za a yi jerin gwanon gangamin ƙin goyon bayam Shugaba Tinubu a Arewa kuma wasu na kusa da shi za su ci amanarsa.
A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Oluwatosin Osho, Ayodele ya fitar, ya ce shugabannin yankin za su hada baki kuma ba za a kalli duk kokarin Tinubu a matsayin komai ba.
‘’Tinubu zai fuskanci matsaloli da dama gabanin 2027 dómin ‘yan Aréwa za su yi masa zańga-zańgar ƙin jiniń sa. Wasu na kusa da Tinubu za su ci amanarsa.
“Duk da duk abin da zai yi, za a yi wata mummunar makarkashíya daga wasu shugabannin Arêwa a kan sa. Zai yi iya kokarinsa amma ba za a gan shi a matsayin komai ba,” inji shi.
Ya bayyana céwa shugaban kasa da mataimakinsa, Kashim Shettima za su samu wasu matsaloli saboda rashin kwanciyar hankali saboda matsalolin da za su taso daga arewa.
Ya yi gargadin cewa za a fuskanci kóma baya a siyasańce da tashin hankali a karo na biyu na gwamnati mai ci.