Kannywood

Yadda Za.a Kawo Gyara A Kannywood – Rahama Sadau

Jaruma Rahama Sadau ta bayyana cewa, babu wani cigaba da masana’antar Kannywood ta samu a 2019

Ta bayyana cewa, yanzu harkar fim din duk ta faduwa ce tunda ba a buga sidi. Sinima kadai ake samun kudi

Jarumar ta roki gwamnati da ta gina Sinimu a kalla guda biyar a garuruwan Arewa don a samu habaka a harkar Fitacciyar jarumar masana’antar fina-finai, ta bayyana cewa babu wani ci gaba da masana’antar fim ta samu a wannan shekarar ta 2019 me shudewa.

Ta yi gargadin cewa, idan har ba a dauki babban mataki ba, to ba za a samu ci gaba a harkar ba.

Rahama tayi wannan kalami ne a wata hira ta musamman da tayi da mujallar Fim. Jarumar kuma Furodusar fim din ‘Rariya’, ta ce, “Gaskiya babu maganar cigaba a masana’antar fim a wannan lokacin da muke ciki.

Saboda idan ka duba gaba daya, idan furodusa yayi fim a wurin yake iya saida fim din – siniman Kano. “Muna da jihohi 19 a Arewa, kuma duk suna kallon fim. A wani lissafi da aka yi, an fi kallon fina-finan Hausa a kan na Kudu.

Amma wannan kasuwar ta lalace, sinimar kawai ake iya kallon fim. “Yanzu, sai dai ka yi fim kawai dan Kano ya kalla. Don haka ka gaya mani ta inda cigaba yake.

Wanda a da kai ka san idan ka yi fim ka buga sidi da fim daya, sai ka yi kudi. Banda yanzu, saboda kowa ja baya yake yi. Babu wanda zai zuba kudinshi yayi fim, kudin su ki fitowa.

Back to top button
error: Content is protected !!