Labarai

Yadda Yaro Ɗan Shekara 17 Ya Kashe Mawaƙiyar Annabi,

A DAREN Lahadi, 10 ga Satumba, 2023 Allah ya ɗauki ran mawaƙiya Hauwa Shu’aibu (wadda aka fi sani da Hauwar Aleebaba).

Mujallar Fim ta samu labarin yadda Hauwa ta rasu sakamakon wani mummunan haɗari da ya ritsa da ita. Mujallar ta gano cewa a daren shekaranjiya Asabar, 9 ga Satumba ne mawaƙiyar da yarinyar da ke yi mata amshi su ka je gidan shehun su, wato Sharu Uba, a unguwar Hotoro a cikin garin Kano.

Bayan sun fito daga gidan, su na bakin titi za su tare abin hawa, sai ƙarar kwana ta zo inda wani yaro ɗan shekara 17 baban sa ya ba shi makullin mota don ya gyara mata waje, shi kuma sai kawai ya ɗauki motar ya tafi yawo da ita. A nan ne ya haɗu da su Hauwa a bakin titi ya buge su ya tura su cikin kwalbati, inda nan take Hauwa ta samu karaya biyu a ƙafafun ta da mummunan rauni a kan ta.

Majiya ta shaida wa wakilin mu cewa ita ma ‘yar amshin ta samu rauni a kan ta wanda ya sa har yanzu ba ta san inda ta ke ba.

Tun a lokacin dai aka kai su asibiti amma a daren jiya Allah ya karɓi ran Hauwa. An yi jana’izar ta a gidan su da ke Jakara, Kano, da misalin ƙarfe 9 na safiyar yau Litinin.

Ita dai Hauwar Aleebaba, tsohuwar mawaƙiya ce a Kannywood, wadda tun ana Sabon titin Mandawari ta ke situdiyon ‘Iyan-Tama Multimedia’ inda Aleebaba Yakasai ya ke kiɗan fiyano, kuma a nan ta samu laƙabin ta na ‘Hauwar Aleebaba’. Muryar ta ta fito a finafinan Hausa da dama.

Daga baya ne ta koma ta na yin waƙoƙin yabon Manzon Allah (s.a.w.).

Allah ya rahamshe ta, amin.

Daga Fim Magazine

 

Back to top button
error: Content is protected !!