Yadda Shari’ar Murja Ibrahim Kunya Ƴar Tiktok Ya Kasance A Kotu.
Yadda Shari’ar Murja Ibrahim Kunya Ƴar Tiktok Ya Kasance A Kotu.
Tauna Aya…
An ƙara gabatar da Murja Ibrahim kunya a gaban babbar kotun Shari’ar Musulunci da ke filin Hoki da ke Zoo Road a Kano tare da ƙarin wasu mutum uku.
Mai Shari’a ya yi umarni a maida Murja Ibrahim Kunya gidan gyaran hali da tarbiyar zuwa mako tsawon guda nan gaba.
Haka nan kuma a gefe guda, an tisa keyar wasu mutum 3 wato Aminu Ibrahim (Aminu BBC) da Sadiq Sharif Umar mai waƙar batsar nan ta ‘A daidai ta nan’ da kuma Ashiru Idris (Mai Wushirya) bisa zargin kalaman batsa a shafin Tiktok zuwa Gidan Yari su ma na tsawon mako 1.
Ana dai tuhumar su da laifukan aikata abubuwan da za su iya ɓata tarbiyar yara masu tasowa, wanda su ka kuma saɓa da sashi na 355 da 356 da kuma 358 na kundin laifuffuka na kotun Shari’ar Musulunci na Jihar Kano.
Murja Ibrahim kunya ta musanta tuhumar da ake yi mata amma abokin burmunta Ashiru Idriss (Mai Wushirya) ya amsa laifin sa nan take.
Daga – NAGUDU TV