Yadda NDLEA Ta Kama Alhazzan Najeriya Da Hodar Ibilis
Yadda NDLEA Ta Kama Alhazzan Najeriya Da Hodar Ibilis
Jami’an hukumar hana sha da fasakwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA), ta kama wasu maniyyata zuwa hajji da dauke da sinadarin Cocine wato hodar Ibilis a Legas.
Jami’an hukumar sun kai samame a otal din Emerald dake unguwar Ladipo a Oshodi a jihar Legas inda wasu maniyyata zuwa aikin hajjin bana a kasar Saudiya suka sauka, jami’an sun tarar da su suna haɗiyar ƙunshin hodar iblis ɗim gabanin shiga jirginsu zuwa kasa mai tsarki ranar Laraba 5 ga Yuni 2024.
A wata sanarwar manema labarai da Daraktan Yada Labarai na Hukumar NDLEA, Femi Babafemi ya fitar, ya shaida cewa wadanda aka kama yayin samamen da hukumar leken asirin ta gudanar sun hada da: Usman Kamorudeen mai shekaru 31; Olasunkanmi Owolabi, mai shekaru 46; Fatai Yekini, mai shekaru 38; sai wata mace mai suna Ayinla Kemi mai shekaru 34.
Mutanen hudu da ake zargin an ajiye su ne a dakuna biyu a cikin otal din inda suka tanadi kwalayen hodar iblis 200 mai nauyin kilogiram 2.20 da zummar hadiye su, lokacin da jami’an NDLEA suka afkawa dakunansu. An gano nau’in ƙulli guda dari daga kowane ɗayan dakunan biyu wanda ya kawo jimlar kunshi 200 na hirar Ibilis, Mutum biyu da ake zargi sun riga sun hadiye kunshi 100 kowannen su.
Da yake yabawa kwamandan, hafsoshi da jami’an hukumar NDLEA reshen jihar Legas, wadanda suka gudanar da aikin, shugaban hukumar, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (Mai Ritaya) ya ce hukumar za ta ci gaba da yada labaran ta domin ganowa. tare da kama miyagu wadanda za su so su fake a karkashin aikin hajji don aiwatar da munanan ayyukansu da ke iya zubar da kimar Najeriya.
Buba Marwa ya kuma bayyana cewa hukumar za ta yi aiki tare da takwarorin ta na Saudi Arabiya don cigaba da fallasa baragurbin Mahajjata tare da hukunta su.