Kannywood

Yadda Na Yi Hanyar Samar Da Waƙar Jarumar Mata – Sunusi Oscar

Fitaccen direkta na Kannywood, Sunusi Hafeez da aka sani da Sanusi Oscar 442 ya ce shine sanadin ƙirƙirar fitaccen sabon waƙar nan ta Jarumar Mata.

Direkta ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Daily Trust a ranar Asabar inda ya ce shi ya fara bijirowa da tunanin sannan ya faɗa wa mawaƙin ya ce ya rubuta baitocin waƙar kuma ya rera ta.

Ya ce, “Ya kamata in yi cikakken bayani a kan batun waƙar da kuma mallakin ta saboda a fahimci abinda ke faruwa.

“Abinda ya faru shine na tuna akwai lokacin da na ke aiki a kan wani fim ɗi na, sai na kira mawaƙin na ce ya same ni a wurin da muke daukan fim ɗin.

“Da ya zo sai na faɗa mishi cewa ina bukatar waƙa amma saboda wani abu daban kuma na biya shi kuɗin aikinsa.

“Ya dauki kimanin shekara guda bai yi aiki da abinda na faɗa masa ba kafin daga bisani ya aiko min da waƙar da WhatsApp, na kammala fim ɗin da nayi niyyar amfani da waƙar a ciki.”

“Wannan shine yadda aka yi waƙar Jaruma ta samu,” a cewarsa.

A batun mallakin waƙar kuma, direktan ya ce, “Idan ka yi amfani da kuɗin ka ka siya wani abu, abun ya zama naka.

“Sai dai abu ɗaya a nan shine; Amma muna da kyakkyawan fahimta tsakanin mu.

“Kamar fuskoki biyu na kwanɗala mu ke. Tare mu me yin harkokin mu.”

Waƙar Jarumar ya yi farin jini sosai bayan Oscar ya fitar da taƙaitacen bidiyon waƙar, ta kuma janyo cece-kuce a arewacin Najeriya saboda gasar rawa da miji da aka yi ta yi da waƙar.

Wasu da dama sun yaba wa waƙar cikinsu har da Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau da Malam Suleiman Salisu Muhammad Mai Bazazzagiya daga Jami’ar Jihar Kaduna.

Kimanin mutum fiye da miliyan biyu ne suka kalli bidiyon waƙar cikin wata ɗaya da fitowar ta wadda ba a saba samun haka ba ga waƙoƙin hausa.

Jarumar Mata waƙar soyayya ce da Hamisu Breaker da Momme Gombe suka rera.

Sanusi Oscar 442 ne ya bayar da umurnin hada waƙar.

Back to top button
error: Content is protected !!