Kannywood
Yadda na samu wasu makudan kudade a cikin watanni 3 kacal – Maryam Booth
Fitacciyar jarumar fina finan Kannywood, Maryam Booth ta bayyana jin dadinta da wasu manyan nasarori guda biyu data samu a cikin watanni uku na shekarar 2019, wanda bisa dukkan alamu zasu kawo mata makudan kudaden shiga.
Maryam ta bayyana haka ne cikin wata hira data yi da jaridar Premium Times, inda tace a yanzu haka kamfanin magin kafi zabo na Ajinomoto ya dauketa a matsayin jakadiyarsa, hakanan ta samu kwangilar yi ma kamfanin sadarwa na Airtel tallace tallace.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Maryma tana cewa babban aikinta a matsayin jakadiyar wannan kamfani shine zata dinga yi musu bidiyo da hotuna don yin tallace tallace dasu, hakanan zata yi amfani da shafukanta na sadarwar zamani wajen tallatasu a duniya.
Jarumar ta kara da cewa harkar neman kudinta bai tsaya nan ba, inda a yanzu haka tana da wani katafaren shagon kwalliya, wanda ma har ta fara horas da dalibai masu son kama sana’ar kwalliya.
“A yanzu muna yi ma dalibai darussa a kwasa kwasan kwalliya daban daban, sa’annan na kara ma shagon girma ta yadda muna gyaran gashi da wankin gashin mata, kuma ana sayar da abinci, duk a cikinsa.” Inji ta.
Sai dai jarumar tace dole ne ta cigaba da fadi tashin neman kudi saboda masana’antar Kannywood tayi kasa matuka, ba’a samun alherin da ake samu a baya, amma duk da haka ba wai ta daina Fim bane, sai dai zata cigaba da hadashi da wasu abubuwan.
Daga Jaridar LeGit Hausa