Kannywood

Yadda Na Fuskanci Kalubale Kan Qasidar Annabi

Yadda Na Fuskanci Kalubale Mai Girman Gaske Kan Kwaikwayon Qasidar Annabi A Shafin Tiktok Ganin Cewa Ni Ba Musulma Bace – Stephanie Dadin Kowa Tayi Bayani.

Jarumar KannyWood Sarah Alicious, Wacce Akafi Sani Da Stephanie Nasir Na Cikin Shirin Dadin Kowa Ta Bayyana Kalubalen Data Fuskanta A Lokacin Da Ta Kwaikwayi Wani Qasidar Annabi A Shafukan Sada Zumunta.

Ta Bayyana Cewa Ta Fuskanci Kalubalen Ne Yayin Da Wani A Shafin Tiktok Ya Tambayeta Kan Cewa Ta Misha Waka Da Larabci, Sai Ta Dakko Wani Bidiyon Qasida Data Taba Hawa Sai Ta Daura Masa.

Hakan Da Tayi Shine Ya Jawo Mata Maganganu Kala Kala Masu Zafi Da Marasa Dadi, Inda Ba Iya Bangaren Musulmai Kawai Ba. Har Bangaren Yan Uwanta Kirista Ta Fuskanci Kalubale Sosai, Inda Tace A Lokacin Haka A Dinga Kiranta Ana Cewa Ta Musulunta, Alhali Kuma Ba Haka Bane..

Ga Cikakken Hirar Da Ayi Da Jarumar Ta Dadin Kowa.

Back to top button
error: Content is protected !!