Labarai

Yadda Mansurah Isah Ta Fashe Da Kuka Saboda Tausayi

KWANAN baya a soshiyal midiya wata mata ta wallafa hoton wani yaro mai suna Halifa mai fama da wata cuta, inda ta riƙa zagin halittar sa, ta na tambayar sa shi mutum ne ko a’a.

A bidiyon, an ji yadda yaron ya na ce mata shi mutum ne, amma ta dage sai ya bar mata gida a dole domin wai ta gaji da ciyar da shi amma ga shi nan ko da yaushe a bushe.

Bidiyon ya ɗauki hankali a soshiyal midiya inda jama’a su ka tausaya wa yaron, tare da neman inda ya ke.

wani bidiyo da tsohuwar jarumar Kannywood Mansurah Isah ta saki cikin takaici  a shafin ta na TikTok, ta nemi duk wanda ya san inda matar ta ke ya faɗa mata za ta ba shi N50,000, idan kuma ya bayar har da lambar wayar ta za ta ba shi N70,000.

A binciken da wani mai rajin taimakon marasa ƙarfi a TikTok, Aminu J. Town, ya gudanar ya bayyana cewa sun gano matar kuma an damƙa ta ga hannun hukuma

cewar sa, tuni yaron ya fara karɓar magani.

A lokacin da Mansurah Isah ta je gidan su yaron don tallafa masa tare da ci gaba da kula da lafiyar sa ta fashe da kuka ganin irin halin da ta same shi a ciki.

Mansurah ta yi alƙawarin  tallafa wa yaron don ganin rayuwar sa ta inganta bayan nema masa lafiya da za ta ci gaba da yi.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa tuni dai wannan yaro ya koma hannun ‘yar kasuwar nan mai taimakon mabuƙata, wato Hajiya Layla Ali Othman, wadda ta ɗauki nauyin kula da rayuwar sa daga yanzu.

Back to top button
error: Content is protected !!