Labarai

Yadda Labarin Hussaina Da Mijinta Abbas Soja Ya Ƙara Fito Da Tasirin New Media

Yadda Labarin Hussaina Da Mijinta Abbas Soja Ya Ƙara Fito Da Tasirin New Media A Idon Duniya

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

Labarin sojan ruwa, Seaman Abbas Haruna wanda matarsa Hussaina Iliyasu ta bayar game da tsare shi da Ogansa, Birgediya Janar MS Adamu ya sa aka yi sanadiyyar saɓa umarni a tashar Brekete, ya ƙara fito da ƙarfi da tasirin New Media wajen yaƙi da zalunci da ƙwatowa waɗanda aka zalunta haƙƙinsu a Najeriya da ma Duniga gaba ɗaya.

Ƴancin da Hussaina da sojoji abokan Abbas masu ɗora ta a hanya suka gaza nemowa cikin shekaru shida da Abbas ya shafe a tsare har ya fara haukacewa, shi ne ya samu cikin kwana ɗaya a sanadyyar Media.

Gwamnati ma ba ta san mai ke faruwa ba amma sanadiyyar wannan hira aMedia hatta ƙaramin ministan tsaro ya ce a bincika, kwamitin kula da harkokin sojojin ruwa na majalissa su ma sun kafa kwamitin bincike. Babban hafsan sojojin Najeriya shi ma ya ce za a yi bincike kuma ba za su saurarawa duk wanda aka samu da laifi wajen wannan zalunci ba. Yanzu haka ma dai wasu rahotannin na nuna cewa an sako Abbas daga inda yake tsare an ba shi dama ya je ya nemi magani. Duk fa Media ce sanadi.

Wannan kaɗai, ya isa ya sa matasa su ɗauki darasi su san yadda za su yi amfani da Social Media ta hanyar da ta dace a madadin amfani da ita wajen zage-zage da shirme ko wasannin da ba su da amfani ba.

New Media ta wuce batun tinƙaho ko alfahari da tarin Followers, batu ne na tayaya za ka yi amfani da tarin Followers ɗin ka gina kan ka tare da buɗewa kan ka ƙofofin arziƙi da damammaki na cigaban rayuwa. Wannan shi ne abin da ya fi dacewa ƴan uwa matasa su maida hankali a kai.

Mutanen da ake musu kallon mahaukata ma ko marasa hankali Midiya ta ɗaga su sun zama wani abu a yau. Ga misalai nan da dama ana gani a zahiri.

Sabbin kafafen sadarwa na zamani (Social Media) da kuma tasirin da su ke da shi wajen samar da sauyi da cigaba a siyasar Duniya gaba ɗaya a wannan ƙarni na ashirin da ɗaya, (21) da muke ciki ya fi gaban misali.

Fasahar sadarwar zamani a yau a iya cewa wata masarrafa ce da ke sarrafa Duniya cikin jagorantar al’amuran rayuwa na al’umma ta kuma taimaka wajen haifar musu da sauye-sauyen cigaban rayuwa mai ma’ana da ɗorewa. A wannan ƙarni na (21), fasahar zamani ta mamaye dukkan rukuni da sassan rayuwar ɗan adam.

Yau a duniya, babu wani wuri da ɗan adam zai boye, duba da yadda ake da fasahar (GPRS) wacce ta ke gano wurare, hatta al’amuran yaƙe-yaƙe yau a duniya ana sarrafawa tare da amfani da fasahohin sadarwa na zamani a kuma samu nasara da galaba kan abokan gaba.

Ba shakka yau duniya ta zama ta zamani ta na tattare a tafin hannu, wacce kuma fasahar sadarwar zamani ita ce tushen wannan nasara da aka samu. Ba wai iya sadar da saƙo kaɗai ko sauƙaƙa zirga-zirga kawai ta ke yi ba, ta taimaka matuƙa wajen jawo nesa kusa ga al’umma ta hanyar amfani da na’urar tauraron ɗan adam da na’ura mai ƙwaƙwalwa ta yadda duk nisan wurin fasahar kan jawo shi ya dawo kusa ba tare da wata tangarɗa ba.

Haƙiƙa Media ta wuce duk yadda muke tunani wajen ƙarfi da tasirin isar da saƙo a samu biyan buƙata. Dan haka ya kamata mu nemi shawarwarin masana da ƙwararru a fagen domin su ɗora mu a kan hanyar da za mu yi amfani da ita mu ci ribarta.

A wannan rubutun na haɗa muku da asalin Hoton MS Adamu sabanin wanda mutane suke yaɗawa.

Back to top button
error: Content is protected !!