Labarai

Yadda Ayi Amfani Da Wata Mata Saboda Ganin Rarara

Matar Da Ta Aaikata ZINA Saboda Ta Samu A Hadata Da Mawaki Dauda Rarara MATAR AURE Ce!

Matar nan da mu ka kawo muku hirar da aka yi ita a wannan shafi na NAGUDU TV kimanin kwanaki 7 da su ka gabata, da ta zo Kano daga Adamawa don ganin mawaki Dauda Kahutu Rarara, wadda har ta yi ikirarin ta bayar da kan ta ga wani dan Fim ya sadu da ita, a matsayin tikitin bude mata kofar da za ta bi don samun ganin mawakin, kasancewar ta babbar masoyiyar sa, daga karshe dai binciken NAGUDU TV ya gano ashe matar aure ce!

Matar mai suna Zainab, wadda yar asalin Mubi ce ta jihar Adamawa, matar aure ce wadda ke zaune a garin Suleja ta jihar Neja tare da mijinta da su ka yi aure tun kusan kimanin shekaru 3 da su ka gabata duk da ba su taba haihuwa ba a tsawon lokacin nan.

Wata majiya ta kusa da ma’auratan wadda ba ta bukatar bayyanawa, ta shaidawa NAGUDU TV cewa, Zainab wadda asalin sunanta Bara’atu ne, ta fara tayarwa mijinta kayar-baya ne bayan shafe fiye da shekaru 2 da auren su ta hanyar fara bullo masa da wasu halayen da ya kasa gane kan ta da gindin ta.

Majiyar NAGUDU TV ta ci-gaba da cewa, babu abun da Zainab ta nema ta rasa na wajiban hakkokin aure, amma haka kawai sai ta tsiri fita daga gidan mijin na ta ba tare da sani ko neman izinin sa ba. Wadda kuma duk iya kokarin da mijin na ta ya yi don taka mata burki kan lamarin abun ya faskara. Domin duk lokacin da ta fita daga gida bai sani ba, idan ya tuhume ta in da ta je, to sai sun samu matsala da ita. Kuma ba zai san in da ta je din ba. Saboda yanayin aikin sa, idan ya fita da safe sai yamma ko dare ya ke dawowa, wasu lokutan ma ya kan bar gari.

Kamar yadda majiyar ta mu ta tabbatar, akwai tasirin zugar kawayen da ta ke tare da su tun kamin ta yi aure, wadda su ke hure mata kunne da tunzura ta wajen saba umarnin mijin na ta a yanzu, duk da auren Soyayya su ka yi da shi na saurayi da budurwa. Amma sai ga shi ta kan furta masa ita ba ta dauke shi a matsayin miji ba, kuma bai isa ya raba ta da kawayen nan na ta ba.

Sannan kamar yadda majiyar NAGUDU TVn dai ta bayyana, akwai wasu daga cikin kawayen Zainab da mijin na ta ya haramta musu zuwa gidan sa ma, saboda irin huduba da hirar da ya ke riskar su na yi a mabambantan lokuta. Kuma hatta ita kan ta Zainab din, ta taba shaida wa mijin na ta yadda wata daga cikin kawayen ta mara aure, da ke gararamba a titi ke ba ta shawarar ta rabu da mijin nata, saboda kasacewar sa ba wani attajiri ba, duk da ya na da rufin asirin da bai gaza daukar nauyin iyalin sa ba. Amma duk da haka, Zainab din ke ci-gaba da mu’amala da ire-iren wadannan kawayen, ba tare da nisantar su ba.

Haka nan kuma dai, a cewar Majiyar NAGUDU TV din, kamin tahowar Zainab zuwa garin Kano neman mawaki Rarara a matsayin ta na masoyiyar sa, har ma ta aikata fasikancin da ta yi ikirarin, dama su na gaban Kotu da mijin na ta, sakamakon k’ara da ta shigar ta na neman Kotu ta raba auren na su. Duk da ba wannan ne karo na farko da ya taba sakin Zainab din ba. Domin a cewar majiyar ta mu, ko a cikin Azumin nan da ya gabata ma, ya saki Zainab din kamin daga bisani ta roke shi ya dawo da ita. Sai dai duk da karar da ta kai shi ta na neman sakin, daga karshe guduwa ta yi ta daina zuwa zaman Kotun a Suleja.

Zainab dai, wadda ta ke zaune a garin Suleja tun kamin ta yi aure, ba ta da wasu dangi ko ‘yan uwa a garin illa kawaye da ta ke tare da su, har zuwa lokacin da mijin ta na yanzun ya gan ta tare da wani abokin sa, ya kuma je har can garin su wato Mubi ta jihar Adamawa aka daura musu aure a haka, su ka dawo Suleja su ka ci-gaba da zama kamin daga bisani kuma ta fara masa botsara.

Majiyar ta NAGUDU TV ta kuma shaida mana cewa, a yanzu dai mijin Zainab ya yanke shawarar kawo karshen shari’ar da su ke yi a Kotu ta hanyar sakin ta kamar yadda ta shigar da kara ta na nema. Domin duk da ya na matukar Son ta, wadda shine dalilin kin sakin ta har ta kai su ga Kotun ma, a yanzu kam zai yi wahala ya iya ci-gaba da zama da ita da irin wadannan abubuwan da ta yi ikirari da bakin ta, ta aikata.

Game da kuma ko Zainab ta na sha’awa da bibiyar son shiga harkar Fim kuwa, majiyar ta Nagudu TV ta bayyana cewa, tun kamin Zainab ta yi aure, ita da wata kawarta, sun dai taba yin tallar shagon tsohuwar jaruma Mansurah Isah na ‘DIS N DAT’ tun farkon bude shi a Kano, idan ban da wannan, babu wani da ya hada Zainab da harkar Fim.

Daga Nagudu TV.

Back to top button
error: Content is protected !!