Labarai

Yadda Amarya Ta K@she Angonta Kan Kudin Cefane A Yobe

Yadda Amarya Ta K@she Angonta Kan Kudin Cefane A Yobe

Wata matar aure ‘yar shekara 22 a jihar Yobe ta kashe mijinta da wuka saboda abinci da kudin cefane.

Tuni dai rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta cafke matar mai suna Zainab Isa bisa zarginta da kashe mijinta, Ibrahim Yahaya, mai shekaru 25.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Yobe, Garba Ahmed, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, DSP Dungus Abdulkarim ya fitar.

Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne a ranar 25 ga watan Yunin 2024 a Damaturu, kuma tuni aka kai Zaina ofishin sashen CID na ‘yan sandan jihar domin gudanar da cikakken bincike tare da gabatar da ita a kotu.

Wacce ake zargin ta amince da aikata laifin, inda ta ce hakan wani mataki ne na kariyar kai a lokacin da wata hatsaniya ta barke tsakaninta da mijinta.

Ta bayyana cewa ana samun tashin hankali a tsakanin ta da mai gidanta tun bayan aurensu, duk da cewa akwai haihuwar ‘ya’ya a tsakaninsu, kuma sau tari rikicin kan kaure ne a sakamakon kudin cefa ne ko kuma abinci.

CP Ahmed ya bayyana alhininsa game da wannan mummunan lamari da ya faru tsakanin ma’auratan wanda ya yi sanadin mutuwar matashin angon, sakamakon rashin jituwar aure.

Wani makwabcin ma’airatan ya shaida cewa fadan da aka yi tsakanin Ibrahim Yahaya da Zainab Isa a gidansu dake unguwar Abbari a Damaturu, inda rigimar ta rikide zuwa tashin hankali, wanda hakan ya sa Zainab ta yi amfani da wuka wajen raunata mijin nata a kirji kafin isowar ‘yan sanda.

Kwamishinan ‘yan sanda Ahmed ya shawarci ma’aurata da su nemi taimako daga hukumomi ko kotuna a maimakon tada kayar baya wajen magance matsalolin aure, inda ya yi kira ga al’umma da su tunkari rikice-rikicen aure cikin hankali duba da irin kalubalen tattalin arzikin da kasar ke fuskanta domin hana su shiga ayyukan aikata manyan laifuka irin su kisan kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!