Yadda Aka Kama Wani Mutum Dauke Da Kokan Kan Mutum A Abuja
Yadda Aka Kama Wani Mutum Dauke Da Kokan Kan Mutum A Abuja
Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, ta kama wani Nuhu Ezra da ke garin Gosa, Lugbe a babban birnin tarayya Abuja,’ dauke da kokon kan mutum da kuma ƙasusuwa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Josephine Adeh, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, 10 ga watan Yuli, 2024, ta ce wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa ya debo sassan ne daga daji a lokacin da yake farauta da niyyar sayar da su a kan kudi ₦600,000.
Jami’an rundunar ‘yan sandan da ke aiki a sashin ‘yan sanda na Iddo ne suka kama wanda ake zargin bayan samun sahihan bayanan sirri. “Da aka yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya bayyana cewa ya dauko su ne daga daji a lokacin da suke farauta kuma ya yi niyyar sayar da su a kan naira dubu dari shida (₦600,000),” in ji sanarwar.
“Kwamishina ƴan sandan babban birnin tarayya Abuja ya ba da umarnin cikakken bincike don tabbatar da wanda ke dauke da sassan jikin, wanda ake sayarwa, da kuma tsawon lokacin da wanda ake zargin ya yi a cikin kasuwancin da ake zargin sa”
Kwamishinan ya bukaci mazauna yankin da su yi taka-tsan-tsan da muhallin su tare da kai rahoto ga ‘yan sanda game da wani abu da suke zargi..