Labarai

Yadda Ɓarayi Su Ka Ci Kasuwa A Wajen Ɗaurin Auren Ado Gwanja

Yadda Ɓarayi Su Ka Ci Kasuwa A Wajen Ɗaurin Auren Ado Gwanja A Ranar Jumma’a

Ranar Juma’a 21 ga watan Yulin 2023 kam dai ɓarayi da ƴan-sanen waya sun ci kasuwa a wajen ɗaurin auren mawaƙi Ado Gwanja a harabar masallacin Juma’a na Jami’ar Northwest University da ke Ƙofar Waika a Kano.

Da farko dai, ango ya baya nan aka ɗaura auren sakamakon makara da su ka yi. Kasancewar ana idar da Sallah misalin ƙarfe 1:10pm aka ɗaura auren. Yayin da shi kuma ango da tawagar sa ba su samu ƙarasowa wajen ba, sai ƙarfe 1:56pm. Wadda wannan ya sa, hatta ɗalibai mata da su ka fito daga na su ɓangaren da su ka yi Sallahr, da dama ba su tafi ba. Sun tsaya jiran zuwan shi.

Bayan da ya iso ne, wuri da ya hargitse, mutane su ka yi caaa a kan shi. Ana wannan turmutsutsun ne, su kuma ƴaƴan na’ayya su ka fara na su aikin. A take a cikin abun da bai wuce ƙasa da mintoci 5 su ka zarewa kusan mutum 5 waya, ciki har da Ni ba tare da mun ankara ba.

Bayan ni, sun sacewa darakta Salisu Mu’azu (Rijiyar Zaki) ta sa shima da kuma Raji Abdullahi da wasu mutum biyu daban da su ma su ke ta kururuwa a wajen.

Bayan wannan, sun sacewa wata mata ma motar ta a bakin gate, sai kuma wani da su ka sacewa Babur (Mashin mai ƙafa biyu) shima dai a wajen.

Don haka da wannan na ke sanar da mutanen da mu ke mu’amala ta Facebook-Inbox da What’sApp, duk wadda ya ga saƙo daga ƙarfe 2 na rana zuwa 9 na daren nan, YAU Juma’ar nan to, ba daga, Ni Ahmad ba ne. Ƴaƴan banzan ne.

Da fatan Allah fitarwa duk wadda su ka zalunta hakkin su, Amin. 🤲

Daga Dan Jaridar Nan – Ahmad Nagudu

 

Back to top button
error: Content is protected !!