Ya Mayar Da 370,000 Da Aka Tura A Asusunsa Bisa Kuskure
Yadda Wani Matashi Abba A. Abdullahi Ya Mayar Da 370,000 Da Aka Tura A Asusunsa Bisa Kuskure.
Sati biyu da suka wuce, Wata ta turo min kudi, 370k nayi shiru iya shiru naji ko za’a kirani ayi min bayanin kudin banji ba, Amma kullum cikin dubawa nake ko zasu zuke kudin su. Amma idan na gansu har dadi nake ji.
Nayi tinanin masu siyan takalma ne, Amma shiru babu bayani. Sai naje banki nayi musu bayani, cewar an tura min kudi amma ba source, suka duba account number din wacce ta turo min kudin, suka ce idan na amince za’a kira sender din.
Aka bani takarda na cike, suka rangada mata kira, shiru bata dauka ba, har na soma tinanin ko zakkah ce dai kudin nan, can sai aka kara kira, aka dauka. Banker din yayi mata bayani ga dalilin kiran, wanda aka tura kudin ne yazo ya dawo miki dashi.
Baiwar Allah kawai naji ta fashe da kuka, wai sati daya tana shan wahala, akan yadda za’a dawo da kudin banki sai wahala suke bata. Ni dai nayi zuru-zuru mutanan banki sai kallona suke.
Aka hadani da matar tana magana tana kuka, ni kuwa nace a zuciyata baiwar Allah dama kin daina kuka ni dai tura miki kudin ki nake so nayi na tafi gida yunwa nake ji.
Ta karbi number ta, sai ta kirani ta layina, tace kafin na saka kudin a account dinta na cire 20k nasha ruwa ta gode. Nace mata to, ni Kuma dana tashi cike teller sai na cike mata kudinta duka, na bar 5k, na tura mata 365k. Shima dai kar ace na mayar da hannun kyauta baya ne. Da duka zan tura mata kudin ta.
Baiwar Allah a wannan rayuwar me yasa zan ci miki kudi har 20k ba wannan maganar, da 1k na dawo gida 4k dabino na siya na dinga bawa almajirai. Hakan ma ai normal ne.
Tana ganin alert ta kirani wai ya haka, ai 20k nace ka dauka, nace mata itama 5k din dana dauka kudin adaidaita ne da nazo, da yunwar azumi da nasha, da Kuma tararrabi da jin dadin kudin da ba nawa ba.
A karshe dai mamana ta dinga suburbudawa addu’a, bani ba. Nace hakan ma normal ne. Amma nayi missing din ganin wannan kudi a account dina.