Kannywood

Ya Kamata Mu Tausayawa Rahama Sadau (Hotuna) – Datti Assalafiy

Daga Datti Assalafiy

Rahama Sadau a mizani na cigaban mai hakan rijiya, hajarta sai kara gaba take yi, duniya ta aure ta sosai, siffarta na Musulunci har ya fara canzawa, ina matukar jin tausayin wannan baiwar Allah.

Duk lalacewar wasu daga cikin matan da suke sana’a irin nata musulmai, iskancinsu bai kai ga fara bayyana da irin wannan mummunan shiga na rashin mutunci alhali suna amsa sunan musulunci ba
Abinda takeyi ba waye bane, kuma ba abin burgewa bane, ya kamata a tausaya mata, sannan ayi mata addu’ah, a dinga jan hankalin iyaye mata musulmai da kada suyi sha’awar rayuwar duniya irin wannan, ko ‘yan boko aqeedah da suke ingizata basa barin kannensu mata suna bayyana da irin wannan mummunan yanayi
Ya Allah ga baiwarKa nan, Allah Kai Ka halicceta, Ya Allah muna rokonKa Ka shiryeta, idan ba mai shir

yuwa bane Allah Ka nesanta wannan dabi’a nata ga sauran musulman Nigeria baki daya. Amin.

Back to top button
error: Content is protected !!