LabaraiUngategored

WATA SABUWA: Ganduje Ya Baiwa Sarki Sanusi Wa’adin Kwana Biyu

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bai wa Sarki Sanusi kwana biyu kacal da ko dai ya amince da nadin da gwamnan ya yi masa a matsayin shugaban majalisar sarakunan jihar Kano ko kuma ya yi watsi da shi.

A wata takarda mai dauke da sa hannun babban sakataren ayyuka na musamman na jihar Kano, Musa Yahya Bichi wadda kuma ke dauke da kwanan watan 19 ga Disamba, gwamna Ganduje ya nemi dole martanin Sarkin ya kai gare shi a cikin kwanaki biyu da karbar wannan takarda.

A lokacin da gwamna Ganduje ya yi nadin dai ya shaida wa sarakuna guda biyar na jihar cewa duk sarkin da ya ki halartar taron sarakuna sau uku ba tare da wani kwakkwaran dalili ba to za a ladabtar da shi ta hanyoyi da dama cikin har da tsigewa.

Sai dai wasu na makusantan Sarki Sanusi sun ce Sarkin bai yi ido biyu da takardar nadin ba ballantana ya mayar amince ko ya yi watsi da mukamin na shugaban majalisar sarakuna.

Wannan dai takarda na zuwa ne kwana daya bayan da Sarki Sanusi da sauran sarakunan guda biyar suka hadu da juna a karon farko.

Rahoton BBC

Back to top button
error: Content is protected !!