Labarai

Wata Da Ba Musulma Ba Ta Jigata Bayan Daukar Azumin Ramadana

Wata Mata Da Ba Musulma Ba, Tayi Yunƙurin Yin Azumi, Ta Jinjina Wa Al’ummar Musulmi Masu Azumi, Bayan Ta Sha Da Kyar

Wata matar aure mai suna Eniola Fagbemi Sisialagbo ta shaida cewa ita Kirista ce, amma mijinta Musulmi ne, kuma tana sha’awar yadda Musulmi ke azumi, domin kullum sai ta tashi lokacin sahur, ƙarfe 4:30am domin shirya wa mijin nata abincin da zai yi sahur, hakan ne yasa ita ma wata rana tace zata jaraba azumin.

Ta ce bayan nayi sahur gari ya waye, “ƙarfe 10 na safe sai cikina ya fara amsawa, amma duk da haka na dage har zuwa ƙarfe 12 sai naga idanuna sun fara jujjuyawa, nan na ɗauki waya na kira mijina na sanar masa halin da nake ciki, ya ce na daure, ko da karfe huɗu tayi na suma sau biyu, sai ganin kai na nayi a asibitin SAANU da ke garin Makola a Ibadan, jihar Oyo, na rantse da Allah wannan azumi da Musulmi ke yi ba wasa ba ne, ina jinjinawa Musulmi masu Azumi.” In ji ta.

 

Back to top button
error: Content is protected !!