Iyalai

Wasu ‘Yan Madigo Sun Kafa Sabon Tarihi A Duniya,

Wasu ‘yan madigo ma’aurata sun kafa tarihi a duniya bayan da suka haifa yaro namiji, Legit na ruwaito.

  • Ma’auratan sun bayyana jin dadinsu ta yadda aka kwashi kwan halittar daya aka dasawa dayar
  • A ranar 30 ga watan Satumba, Donna wacce itace matar ta sullubo musu yaro namiji

Wasu ‘yan madigo da suka yi aure sun kafa tarihi. Sun bayyana yadda suka yi wa juna ciki, suka raineshi kuma suka haifa.

Ma’auratan ‘yan madigon sun yi maraba da jaririnsu ne da suka haifa a watanni biyu da suka gabata. Jasmine Franscis Smith ce ta haifeshi bayan da aka yi amfani da kwan halitta aka dasa shi a mahaifar matar mai suna Donna.

Wani asibitin da ke Landan ne ya taimakawa ma’auratan. An karba kwan halitta daga daya, inda aka dasawa matar a mahaifarta har ta yi raino kuma ta haihu.

Su ne na farko a duniya da suka fara yin irin hakan, duk da ma’aurata ‘yan madigo da yawa sun haihu ta hanyar dashen kwan halitta. Amma duk yadda ake dabarun, sai dukkan ma’auratan sun bada gudummawarsu.

Lance Cpl Donna Franscis-Smith mai shekaru 30 a duniya ta sanar da jaridar Telegraph cewa: “A gaskiya muna cikin matukar farinciki. Mun yi ciki kuma mun haifeshi duk da muna jinsi daya. Mun bada gudummuwa dukkanmu a samar da jaririn. Mun tallafawa juna kuma mun cimma manufarmu.”

“Kwan halitta na ne kuma daga jikina aka cireshi. An maido min shi mahaifata inda yayi kusan sa’o’i 18 kafin a mayar dashi zuwa mahaifar Jasmine. A hakan ta dau cikin har ta haifeshi.”

Jasmine mai shekaru 28 ce ta haifa dan su a ranar 30 ga watan Satumba a Colchester Essex, inda ma’auratan ke zama.

Ma’auratan sun yi aure ne a watan Afirilu na shekarar da ta gabata bayan da suka hadu a 2014 ta yanar gizo.

Back to top button
error: Content is protected !!