Kannywood

Wani Ya Musulinta Saboda Kallon Izzar So

Fim din Izzar So ya sanya wani mutumi dan asalin jihar Cross Rivers ya karbi addinin Musulunci, yayin da mutane da yawa ke kushe ‘yan fim…

A yayin da mutane da dama suke yiwa ‘yan shirin fina-finan Hausa na Kannywood kallon mutane dake bata tarbiyya da kuma lalata al’ada, sai gashi an samu wani mutumi ya karbi addinin Musulunci sakamakon kallon fim da yake yi.

Wani rahoto da muka ci karo dashi a shafin Facebook na Kannywood, ya nuna yadda wani bawan Allah ya canja addini zuwa addinin Musulunci sakamakon kallon fim din Izzar So da yake yi.

Mutumin da aka bayyana sunan shi da John, ya fito tun daga karamar hukumar Idom dake cikin jihar Cross Rivers, domin ya karbi kalmar Shahada, inda daga baya ya canja sunan shi zuwa Umar.

A bidiyon da shafin na Kannywood ta wallafa an nuno mutumin tare da shahararren jarumin nan Lawal Ahmad da kuma wasu mutane a lokacin da ake karanta masa kalmar shahada yake biyawa, inda a kasan bidiyon aka yi rubutu kamar haka:

“Masha Allah A Yaune Mukayi Babban Kamu A Musulunci Inda Wannan Bawan Allah Ya Shiga Musulunci Saboda Kallon IZZAR SO Da Yakeyi, Tun Daga Cross river, idom Ikon Local Government Cross River Yanzu Haka Dai Ya Karbi Musulunci, Kuma Yanzu Haka Sunansa Ya koma Umar Daga John, Munayi Masa Addu a Allah Yasa Ya shigo Addinin musulunci A Sa a Allah Yasa Ya Amfane Shi, Amin.”

Ga dai bidiyon yadda lamarin ya kasance:

Shirin Izzar so dai shiri ne mai dogon zango da yake tashe a wannan lokaci, wanda jarumi Lawal Ahmad yake shiryawa.

A baya dai dama jarumi Falalu Dorayi ya taba yin wata magana da yake nuni da cewa akwai mutane da dama da suka karbi addnin Musulunci sakamakon kallon fim din Haussa da suke yi.

Sai dai wannan magana ta jarumin ta tada kura, inda mutane a shafukan sadarwa suka yi caa suke ganin wannan magana ta jarumin sam ba haka take ba, domin a ganin su, babu abinda jaruman suke yi idan ba bata tarbiyya da al’adar al’ummar Hausa da Musulmai ba.

Mun Samo Wannan Labarin Daga Shafin LabarunHausa

Back to top button
error: Content is protected !!