Labarai

Wani Mutum Ya Saki Matarsa Sabo Da Tsananin Kyawunta Yayi Yawa

Wani Mutum Ya Saki Matarsa Sabo Da Tsananin Kyawunta Yayi Yawa

Daga Suraj Na’iya Kududdufawa.

Wani mutum ya kai matarsa kotu kuma ya sake ta a gaban alkali sakamakon tsananin kyawunta ya yi yawa.

Wannan lamari ya faru ne a kasar Zimabgwe inda mijin matar mai suna Arnold Masuka mai shekaru 40 yanzu shi kwata kwata matarsa ta ficemasa a ransa baya bukatar ci gaba da zama da ita.

Arnold ya bayyanawa alkali cewar sabo da tsabar kyawun matarsa idan yana kallonta baya iya bacci da daddare ko da yanajin baccin.

Ya kara da cewar wani lokacin har tsoron fita wajen aiki ya keyi sakaakon kada wani ya kwacemasa ita wato ya zauna zaman gadinta.

“Rashin bacci na sabo da tsabar kawunta da kuma zaman gadinta da keyi sun zamemin masifa, kawai gara na sake ta na huta ko na samu sauki” cewar Arnold.

Matar mai suna Hilda Mleya mai shekaru 30 maza da yawa sun nemi aurenta amma ta nace ita Arnold ta keso ta aura.

Shi kansa alkalin mai suna Henry Chidvidzo da ya karbi batun shara’ar ya bayyana cewar bai taba gamuwa da irin wannan lamari mai abin mamaki kamar wannan lamarin ba domin abin ya dauremasa kai

Back to top button
error: Content is protected !!