Kannywood

Wani Matashi Yasha Fiya Fiya Akan Maryam Yahaya

Wani matashi mai suna Kamal daga garin Gashua a jihar Yobe ya yi tattaki zuwa jihar Kano don ganin jaruma Maryam Yahaya

Bayan kwashe kwanakin da matashin yayi a Unguwar Zoo road don ganin jarumar amma babu nasara, ya sha fiya-fiya a cikin fura

Hukumar Hisbah ta aika da mota inda aka kwashi saurayin zuwa asibiti har aka ceto rayuwarsa

Wani matashi da ya zo daga Yobe ya sha fiya-fiya saboda bai samu ganin Maryam Yahaya ba.

Wani matashi da ya yi tattaki tun daga jihar Yobe da ke yankin arewa maso gabas na kasar nan, don ganin jaruma Maryam Yahaya, ya so yayi ajalin kansa saboda rashin cikar burinsa na ganin jarumar ta shi.

Kamar yadda jama’ar da ke wurin suke bayyanawa, matashin ya kwana a Unguwar Zoo road, inda ya zama kamar dandalin taruwar jaruman Kannywood don ya ga jaruma Maryam Yahaya amma bai samu ganin ta ba.

Hakazalika, an ji wasu na cewa sau uku matashin ya yi yunkurin shan fiya-fiya, kafin daga bisani ya bulbulawa cikin sa maganin kashe kwari da ya kusa zama ajalinsa.

An dai samu ceto rayuwar matashin ta hanyar bashi agajin madara.

Sai dai duk da wannan abu da ke faruwa, Jaruma Maryam Yahaya bata san yana yi ba ko kuma ta yuwu bata samu koda labari ba.

Koda kuwa ta samu labari, bata yi yunkurin yin wani abu a kai ba domin ko a shafinta na sada zumunta bata nuna alhini ko jaje ga wannan dan kasadar ba da ya so salwantar da rayuwar shi saboda ganin ta ba.

Bayan duk kokarin ganinta da yayi amma hakan ya gagara, ya yanke shawarar buga waka, ta yuwu ta hakan zai samu su hadu cikin sauki.

Sai dai hakan ya tashi a tutar babu. Daga nan ne ya sha fiya-fiya a cikin fura inda ya fadi rai a hannun Allah.

Babu jimawa hukumar Hisbah ta aiko da mota inda aka kwashe shi zuwa asibiti don ceto rayuwarsa.

A zantawar Dala FM da saurayi Kamal bayan farfadowarsa a asibiti, ya ce a halin yanzu ya hakura amma fa son Maryam Yahaya na nan a ransa daram.

One Comment

Back to top button
error: Content is protected !!