Labarai
Wani Matashi Ya Fara Tattaki Zuwa Kaduna Domin Jinjina Ma El Rufai
Matashi Ya Soma Tattaki A Kafa Daga Jihar Yobe Zuwa Kaduna Domin Jinjinawa Gwamna Elrufai Kan Yadda Ya Jajirce Wajen Kafa Dokar Hana Zirga-zirga A Kaduna Don Gudun Yaduwar Cutar Corona
Matashin mai suna Ahmed Isa wanda ya soma tattakin tun a jiya Alhamis, ya bayyana cewa ya yi matukar yabawa Gwamna Elrufai kan yadda ya jajirce wajen ganin doka ta yi aiki don gudun yaduwar cutar corona a fadin Kaduna.
Ahmed ya ce dokar wadda Gwamnan ya saka ya yi ne don kaunar jihar Kaduna da al’ummar ta da yake yi, amma sai mai hankali da tunani ne zai gane hakan.
Daga Aliyu Ahmad