Labarai

Wani matashi Mai shekaru 38 ya yanka rago da canza sunan sa zuwa Muhammad Buhari

An gudanar da bikin sunan wani matashi mai shekaru talatin da takwas a Duniya a nan Kano daya sake sunan sa zuwa sunan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Matashin mai suna Muhammad Ibrahim dake Unguwar Gidan zoo yace ya canza sunan sa ne sakamakon kaunar da yake yiwa shugaban Kasa Buhari wanda hakan yasa ya siyo katon Rago ya yanka ya kuma rarraba Alewowi ga mutanan da suka halarci taron bikin sauya sunan nasa daya gudana a yau zuwa na shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Matashin daya sauya sunan sa zuwa na shugaban kasa Buhari yace ko kadan ba siyasa ce tasa ya sauya sunan sa daga Muhammad Ibrahim zuwa Muhammad Buhari ba , ya sake sunan sane saboda zunzurutun kaunar da yake yi ga Buhari , bugu da kari kuma kowa yasan Shugaban kasa Buhari ba Barawon dukiyar al’ummar Najeriya bane.

Muhammad Ibrahim daya sake sunan sa zuwa Muhammadu Buhari yace zai canza sunan duk wasu muhimman takardunsa da suke dauke da tsohon sunan sa zuwa sabon sunan sa domin ya cigaba da amfani dasu , duk da cewa shi dan kasuwa ne dama.

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito cewa mutane da dama ne suka halarci bikin sake sunan Muhammad Ibrahim zuwa sabon sunan sa a yanzu wato Muhammad Buhari.

Back to top button
error: Content is protected !!