Kannywood

Wani Malami Ya Harsala Adam A Zango, Karanta Murtaninsa Akan Malamin

Fitaccen jarumin nan na fina-finan Hausa Adam A. Zango ya karyata wani ‘malami’ da ya yi ikirarin cewa jarumin yana neman mata ‘yan kasa da shekara 20 da zummar tantance su domin ya sanya su a wani sabon fim dinsa.

Malamin, wanda aka nuno shi a wani bidiyo yana huduba, ya ce jarumin ya fice daga masana’antar Kannywood ne saboda ba ya so hukumomi su tace fina-finansa da niyyar bin tsarin “tarbiyyar addinin musulunci”.

Ya ce jarumin yana neman mata ‘yan kasa da shekara 20 domin ya sanya su a fim da zummar lalata tarbiyarsu da kuma hana hukumomin tace fina-finai yin aikinsu.

Binciken da BBC ta yi dai ya nuna cewa jarumin ya fita daga Kannywood ne saboda “musgunawar da yake zargin ana yi wa ‘yan fim da mawaka a jihar Kano” inda hukumar tace fina-finan jihar ta kama wasu daga cikin su kwanakin baya.

A bidiyon da Adam Zango ya wallafa domin martani ga malamin, jarumin ya dauki Alkur’ani mai tsarki, ya zargi malamin da “yin karya a kan abin da bai sani ba.”

“Na rantse da Allah duk abin da [malamin] ka fada a kaina karya ne. An yi audition [tantance mutanen da za su shiga fim] a masana’antar Kannywood fiye da sau 100 amma ban taba yi ba.

Duk yarinyar da ka ga na saka a cikin fim dina ita ta kawo kanta ko kuma na ga wasu sun saka ta a fim ni ma na sanya ta. Idan kuma sabuwa ce ta kawo kanta sai na tabbatar da izinin iyayenta kafin na saka ta.”

Jarumin ya kalubalanci malamin da ya fito da shaidar cewa yana kai ‘yan mata cikin otal-otal.

Ya kara da cewa yana sanya mata a cikin fim dinsa ne domin kada su je su yi karuwanci ko su lalace.

Adam Zango ya yi kira ga manyan malami irin su Sheikh Ahmad Gumi da Sheikh Ibrahim Daurawa da Sheikh Abubakar Giro Argungu, wadanda ya ce ba za su yi wa’azi irin wannan a kan sa ba tare da hujja ba, da su ja masa kunne.

NgHausa

I am YusHau Uba, CEO/Founder Of HausaMini.Com.Ng
Back to top button