Ungategored

Wakokin Hausa Guda 10 Da Sufi Shahara A Shekarar 2018


Wadannan Sune Wakoki 10 Da Suyi fuce a Shekarar 2017 

Wakokin da su ka fi yin fice duk na zamani ne wadanda ake kidan su da fiyano, maimakon na gargajiya da ake kadawa da kalangu ko goge ko kukuma ko jauje da sauran su.
Wato a yayin da manyan mutane kan saurari su Shata da Dankwairo da Barmani Choge da sauran su, yawancin matasa sun ta’allaka ne kan sauraren wakoki na zamani.
A binciken neman wakoki da su ka fi yin fice a bana, mun gano cewa wakoki biyu ne su ka shiga cikin goman, yayin da wakoki biyu na Hip-hop ne, sannan an samu mawakiya mace guda daya wadda wakarta ta shiga cikin jerin wakokin 10.

1. ‘Mariya’- Umar M. Shariff (tare da Khairat Abdullahi)- daga fim din ‘Mariya

Wakar ‘Mariya’ ta fito ne a fim din ‘Mariya’ na darakta Ali Nuhu.
Fitaccen mawaki Umar M. Shariff ne ya rera ta, tare da Khairat Abdullahi.
Mawakin, wanda kuma jarumi ne, shi ya fito a fim din tare da jaruma Maryam Yahya a matsayin jaruma.

Wakar Mariya ta Umar M Shariff

‘Mariya’ shi ne fim na biyu da jaruman su ka fito tare a matsayin masoya, kamar yadda su ka fito a fim din ‘Mansoor’.’Mariya’ waka ce ta saurayi da budurwa.
A cikin ta, Umar da Khairat sun nuna kwarewa wajen zuba kalmomin soyayya da shauki.
An yi ittifaki da cewa babu wata wakar soyayya da ta yi fice kamar ta a bana, domin mashirya bikin aure ko na suna da kuma a makarantu sun yi amfani da ita sosai wurin nishadantar da mahalarta.

2. ‘Love’- ALI ISAH JITA

Wannan waka ta zo da wani salo wanda ba a san Ali Jita da shi ba, inda ya rika yin ingausa, wato hada kalmomin Ingilishi da na Hausa.
Wakar soyayya ce wadda a cikin ta mawakin ya girgiza masoyan sa da kalmomi masu ratsa zukata ta yadda duk wanda ya ke cikin nishadi irin na soyayya sai ya ji kamar shi ke furta kalaman da ke cikin ta.

Wakar Love ta Ali Jita

Ali Jita ya kaddamar da wakar ne a otal din Transcorp da ke Abuja kwanan baya.
Matasa da dama sun yi ta daukar bidiyo na kan su, su na bin wakar, su ba turawa a shafin su na Instagram.

3. ‘Shimfidar Fuska’ – HAMISU BREAKER DORAYI

Hamisu Breaker Dorayi sabon mawaki ne wanda tauraruwar sa ta yi haske musamman daga shekarar 2017.
A yau, ya na daya daga cikin mawakan da ke tashe, har wasu ma su na fadin cewa daga Umar M. Shariff sai shi a fagen waka.

Wakar Shimfidar Fuska ta Hamisu Breaker Dorayi

Farin jinin da wakar ‘Shimfidar Fuska’ ta yi, shaida ce ta bunkasar da Breaker ya yi a bana.
Wakar, wadda ta soyayya ce, ta yi tasiri musamman a wurin mata; duk inda ka shiga za ka ji mata su na sauraren ta, saboda kalaman da ya yi amfani da su ga masoyiyar tasa.

4. ‘Gambara’ – ADAM A. ZANGO

Fitaccen mawaki, darakta kuma jarumi Adam A. Zango ya yi wannan wakar ‘Gambara’ ne a kan irin matasan Hausawan nan masu cewa ba su sauraren wakokin Hausa sai na mawakan kudancin Nijeriya ko na kasashen waje.

Wakar Gambara ta Adam A Zango

Sannan ya yi hannun-ka-mai-sanda a kan wasu masu kin jinin ‘yan fim din Hausa har ba su son ganin su, inda ya yi kamar zai antayo ashar amma sai ya kauce.
Ta wani bangaren kuma, wakar zambo ce da ya yi a kan wasu wadanda ba a san ko su waye ba, shi ya sa ma ya kira ta da sunan ‘Gambara’.

5. ‘Girgiza Nan’ – ADO ISA GWANJA da ADAM A. ZANGO

‘Girgiza Nan’ wakar hadaka ce da fitattun mawaka su ka rera.
Wakar ta yi wa gayu dadi, musamman masu A Daidaita Sahu ko Keke NAPEP.

Wakar ‘Yan mata girgiza nan ta Ado Gwanja da Adam A Zango

A tsawon watanni, da wuya ka shiga A Daidaita Sahu har ka sauka ba ka ji wakar ba.
A wakar, shi Ado Gwanja ya na kambama kan sa ne, shi kuma Adam A. Zango ya na yi wa Allah godiya ne.
A wani bangaren kuma, kamar wakar batsa ce, saboda karin ta ba ”Yan Mata Girgiza Nan”.

6. ‘Baba Buhari Dodar’ – DAUDA ADAMU KAHUTU (RARARA)

Fitaccen mawakin siyasa Dauda Adamu Kahutu, wanda ake yi wa lakabi da Rarara, ya yi wakar ‘Baba Buhari Dodar’ ne bayan ficewar wasu manyan ‘yan siyasa daga jam’iyyar APC ta Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, inda ya yi masu zambo.
Masoyan Rarara sun ji dadin wakar, musamman ganin cewa ya dan jima bai yi wa Buhari sabuwar waka ba.
Duk inda ka shiga za ka ji wakar ake ji.
Shagunan masu saida wakoki da finafinai sun sha tambaya kafin wakar ta fito kasuwa.
Yawancin wadanda su ka samu wakar, a intanet su ka same ta.

Wakar Baba Buhari Dodar ta Dauda Kahutu Rarara

Don yayata wakar, Rarara ya sa gasar rawa, inda duk wadanda su ka shirya bidiyon rawa da wakar za su tura a shafin su na Instagram, sannan ya hada da shafin jarumi Adam A. Zango.
Daga nan kuma har zuwa lokacin da aka sa za a gama gasar.
Nan fa matasa maza da mata su ka yi ta tura bidiyoyin rawar da su ka yi da wakar.
Da lokacin da ka sa ya yi, a wani bikin fidda gwani da aka yi a Katsina alkalan gasar sun zabi 10 daga cikin bidiyoyin, daga nan aka tantance har aka samu na 1, na 2 da na 3.
Na farko sun samu kyautar mota kirar Honda EOD, na biyu kuma Keke Napep, na uku kuma mashin kirar Jinchen.

7. ‘Matan Zamani’ – NURA M. INUWA da ZUWAIRA ABDULSALAM

Fitaccen mawaki Nura M. Inuwa ya yi wakar ‘Matan Zamani’, wadda aka saka ta a wani fim mai suna ‘Matan Zamani’.

Wakar Matan zamani ta Nura M Inuwa da Zuwaira Abdulsalam

Jarumi Garzali Miko, Maryam Yahya, Zee Pretty da wasu ‘yan mata biyu su ka hau wakar. Wakar soyayya ce irin ta matan zamani.
Mawakin ya yi amfani da kalamai masu sanyaya zuciya kamar yadda aka san shi da yi.
Wani abin burgewa shi ne yadda mawakin ya sauya salo a tsakiyar wakar, ta yadda in ka fara jin wakar, wani ya zo a daidai wannan lokaci ba zai tunanin wakar ba ce.
Ga shi wakar ta samu sauti mai dadi.

8. ‘Haba’ – MUSA MORELL

Wakar ‘Haba’ ta Morell ce kan gaba a bana a rukunin wakokin Hip-hop.
Wakar ta yi fice tun kafin mawakin ya fitar da cikakkiyar ta a shafin sa na YouTube.

Wakar Haba ta Musa Morell

Duk inda ka shiga yara da manya za ka ka ji su na zolayar juna da wakar; da mutum ya hango abokin sa, sai ka ji ya ce masa, “Hannu daya a sama!”Ita ma wakar ‘Haba’ masoyan Morell sun yi ta daukar bidiyon kan su da ita, su na sakawa a Instagram.

9. ‘Tafi’ – HADDY RAPIA

Haddy Rapia mawakiyar Hip-hop ce da ke zaune a garin Kaduna.
Ta yi wakoki da dama, amma ba irin na nanaye da aka san mata mawaka su na yi ba. Wakar ‘Tafi’ ta yi tashe a musamman a Instagram da YouTube.

Wakar Tafi ta Hadi Rappia

Jigon ta shi ne koda kai, inda mawakiyar ta kambama kan ta.Haddy Rappia ta na kokari sosai, domin ana iya cewa a yanzu babu mawakiyar Hip-hop ta Hausa kamar ta.

10. ‘Da Sauran kallo’ – ISAH AYAGI

Isah Ayagi ya na daya daga cikin sababbin mawakan da ke tashe a wannan zamanin.
‘Da Sauran Kallo’ waka ce ta soyayya wadda babu muryar mace a cikin ta.

Wakar Da Sauran Kallo ta Isah Ayagi

Mawakin ya zazzaga kalaman soyayya da ya ke nuni da cewar ya na yi wa masoyiyar sa ne.Wakar ta yi tasiri a wurin masoya. Duk mai sauraren wakar zai iya samun sanyin zuciya a game da masoyiyar sa idan ya saurare ta.
DAGA IBRAHIM SHEME DA ABBA MUHAMMAD
Daga BBCHausa .COM

Back to top button
error: Content is protected !!