Kannywood

Wakokin Hausa Guda 10 Dasu Shahara A Shekarar 2019

A yayin da shekarar 2019 ta kare inda saura kwanaki kadan ga masu tsawon rai, mawakan Hausa da dama sun yi kokari wajan fitar da wakoki masu daukar hankali a wannan shekarar me karewa, dan hakane shafin hutudole yazo muku da wakoki 10 da suka fi shahara a 2019 a mahangarmu.

Ta 10. Da Tuni baba yaci zabe>>Rarara

Wakar Dauda kahutu Rarara wadda yayi bayan da hukumat zabe me zaman kanta,INEC ta daga zaben shugaban kasa na shekarar nan inda yake cewa, Da yanzu an gama, da tuni baba yaci zabe, ta dauki hankula sosai kuma an jita kamar ba za’a daina.

Siyasa ta taimakawa wannan waka shahara dan haka ta zo mana a ta 10.

Ta 9. Kumatu>>DJ Abba

Wannan waka daga shahararren mawakin gambara daga Arewa, DJ Abba ta dauki hankulan matasa sosai inda ta zama abar so da rerawa, “I wonder Wonder, Why she call my Number, Rai ya baci, Hankali ya tashi, Kai ya dau Chaji, Ban gani in fashi”

Soyayyar da matasa kewa wannnan waka yasa ta zo mana ta 9.

Ta 8. Kogin Zuma>>Garzali Miko

Wakar Kogin Zuma ta tauraron mawakin Hausa, Garzali Miko ta Kogin zuma ta dauki hankula sosai tsakanin matasa maza da mata, tana daga daga cikin wanda ba zaka ce koda sau daya baka taba jinta ba.

Ta 7. Hafeez>>Umar M. Shareef

Wakar tauraron mawakin Hausa, Umar M. Shareef ta Hafeez ta kayatar sosai, duk da cewa mawaka da dama sun yi Hafeez amma ta M. Shareef takenta dabanne inda yake cewa, “Hafeez gani Nazo, Bani in baki, Zabi, ke na Zabo mu yo rayuwa”

Dadi da karbuwar wannan waka tasa tanzo mana a ta 7.

Ta 6. Cypher>>DJ Abba, Lilprince, Jigsaw, Teeswag.

Wakace da ta dauki hankula sosai, ko da wanda basa jin irin wakokin sun saurareta da dama Akwai abokina da yayi ta damuna akan wakar lokacin ban santa ba, shi ya sani na fara saurarenta kuma ta samu karbuwa sosai, Wai tsaya, ka taba mata Dinki ko? Wata bakar jalabiya da Indigo? Tana yawan Forming Nicky ko? Amma Dodo wajan cin girki ko?

Ta 5. Karki Manta Da Ni>>Abdul D One

Matashin mawaki, Abdul D. One yayi kokari wajan yin wakar karki Manta Da Ni, wakace da idan kana jinta zata kashe maka jiki ta sakaka cikin shauki, ta fi dadin saurare idan kana tare da masoyi ko masoyiya ko kuma da dare, “Soyayyar ki ni sai na Fadaaa, banga irin taba”.

Ta samu karbuwa sosai shi yasa ta zo mana a ta 5.

Ta 4. So Da Amana>>Garzali Miko.

Garzali Miko yayi kokari sosai a shekarar 2019 saboda ya saki wakokin da suka dauki hankula suka shahara sosai, So da Amana na daya daga ciki, banda wakar, rawar cikin wakar ma ta kara sayar da wakar a tsakanin matasa.

Ta 3. Na Yi Sa’a>>Hamisu Breaker.

Hamisu ya koma gefe ya shiryo wakar Na yi Sa’a wadda ta cewa wakoki da yawa, Kai kauce( ta bakin Nomiss Gee) inda da wuya koda baka ji wannan wakar ba kai kadai ace baka ji wani yana jinta ba.

Ta 2. Wanda Bai so>>Nura M. Inuwa

Fasihin mawaki wanda in ya furta sai an saurara, Nura M. Inuwa ya saki wakar Wanda Baiso data ratsa tsakanin matasa, Dattijai, kai har ma da Usta zai, dan bazan manta ba akwai wani abokina da Ustazne, yawanci wayarshi karatune amma yana da wakar Wanda baiso ta Nura M. Inuwa a wayarsa. Akwai da yawa wanda waka bata damesu ba amma sunji wannan wakar.

Ta 1. Abba Gida-Gida Abba>>Tijjani Gandu

Bawai dan dadin wakar ko goyon bayan wani dan siyasa ba, Wakar Abba Gida-Gida ta karade Dukkan Arewacin Najeriya saboda salon da siyasar Kano ta dauka a lokacin zaben gwamnoni, inda kuma ta samu martani da kuma sauyawa zuwa kala-kala.

Wannan shine yasa ta zo mana a ta 1.

Back to top button
error: Content is protected !!