Waiwaye: Manyan jarumai 5 mata na Kannywood da su kayi tashe a baya
Kannywood ta cika da ‘yan wasa mata masu tsananin hazaka. Wannan hazakar ce kuwa ke sa su yi suna tare da fice. Masana’antar ta yi sama da shekaru 20 da kafuwa. Da yake duniyar yayi ce, jarumai kan ja zarensu inda daga baya wani abu ke giftowa su bar masana’antar ko su koma baya wasu kuma su dasa a kai.
Ga kadan daga cikin jarumai mata na masana’antar da suka yi tashe kuma aka yi yayinsu a da.
- Fati KK
Tsohuwar jarumar ta masana’antar Kannywood ‘yar asalin karamar hukumar Kontagora ce a jihar Neja. Babu shakka a wancan lokacin tana sahun gaba a jarumai mata na masana’antar. Fati ta bar fim ne tayi aure kuma bata kara dawowa ba. A halin yanzu tana da yara uku. Ta fito a fina-finai irinsu Aure ko Boko, Ban saketa ba, Ina mijina, Mijin hajiya, In da rai da sauransu
2. Hafsat Shehu
Ta bar masana’antar ne inda ta auri wani jarumin masana’antar mai suna Ahmad S. Nuhu. Nuhu ya rasu ne a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a titin Azare zuwa Maiduguri a 2007. An ruwaito cewa, Hafsat ta auri wani dan kasuwa a Abuja amma auren bai yi tsayi ba. A cikin kwanakin nan ne ta sake wani sabon aure. Ta yi auren ne a ba-zata. Don kuwa kwatsam hotunan bikin suka bayyana
3. Mansura Isah
Mansura Isah ta fara aiki da masana’antar ne a matsayin mai bada umarnin bidiyo. Ta fada wasan kwaikwayon ne shekaru 1990s. Kamar dai sauran, ta bar masana’antar ne inda ta auri fitaccen jarumi Sani Danja a 2007. Yana daya daga cikin manyan jarumai maza a masana’antar. Suna da yara hudu a halin yanzu. Ta bayyana a fina-finai irinsu: ‘Yan mata, Jarumai, Zazzabi da sairansu
4. Samira Ahmad
Samira Ahmad jaruma ce da ta yi tashe a wancan lokacin. Itama kamar sauran, ta bar masana’antar ne inda ta auri wani jarumi mai suna TY Shaban, wanda yayi suna a rawa da kuma shirya fina-finai. Ta daina bayyana a fina-finai ne bayan da ta yi aure duk da kuwa ta rabu da jarumin. Ta fito a fina-finai irinsu: Namamajo, Zanen Dutse, Duniyar mu, Zaman aure da sauransu
5. Sadiya Muhammad
An fi sanin jarumar da Sadiya Gyale. Ta fara wasan kwaikwayo ne a 2001 inda har ta kai ga zama fitacciya a masana’antar. Ta auri Alhaji Muhammad Abubakar wanda a yanzu marigayi ne. Ta fito a fina-finai irinsu: Kugiya, ‘Yar fim, Balaraba da sauransu.