Wadanda Su Rasu A Masana’antar KannyWood A Shekarar 2023
Shafin Mujallar Fim Ta Lissafa Wasu Daga Cikin Mutane Masu Alaƙa Da Masana’antar KannyWood Waɗanda Su Riga Mu Gidan Gaskiya A Shekarar Daya Gabata Na 2023.
Litinin, 16 Ga Watan Janairu
Allah ya ɗauki ran jarumin barkwanci a Kannywood, Kamal Aboki, sanadiyyar haɗarin mota da ya ritsa da shi a kan hanyar Maiduguri zuwa Kano.
Litinin, 23 Ga Watan Janairu
Allah ya ɗauki ran jarumi kuma furodusa a Kannywood, Abdulwahab Awarwasa. Ya rasu a garin Jos, bayan ya sha fama da rashin lafiya.
Litinin, 23 Ga Watan Janairu
Allah ya yi wa Khalid ɗan tsohon shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), rasuwa, a wani asibiti da ke ƙasar Ghana.
Alhamis, 16 Ga Watan Maris
Hajiya A’isha Salisu, mahaifiyar darakta a Kannywood, Sadiq Hussaini Jeep, a Kano.
Lahadi, 19 Ga Watan Maris
Dakta S.U. Garba, mahaifin jarumar Kannywood, ya rasu a gidan sa da ke Minna, Jihar Neja.
Litinin, 24 Ga Watan Afrilu
Allah ya ɗauki ran shahararriyar ‘yar wasan kwaikwayo Hajiya Balaraba Tanko, a gidan ta da ke Tudun Wada, Kaduna.
Talata, 25 Ga Watan Afrilu
Malam Muhammad Barde, mahaifin furodusa a Kannywood, Alhaji Habibu Barde ya rasu a asibitin Federal Medical Centre da ke Azare, Jihar Bauchi.
Litinin, 8 Ga Watan Mayu
Jarumin Kannywood, Malam Aminu Muhammad (AZ), ya rasu a asibitin Nassarawa da ke birnin Kano.
Lahadi, 25 Ga Watan Yuni
Marubuci kuma abokin ‘yan fim, Alhaji Auwal Garba Ɗanbarno, ya rasu sanadiyyar haɗarin mota da ta ritsa da shi a garin Jogana da ke Ƙaramar Hukumar Gezawa ta Jihar Kano.
Alhamis, 13 Ga Watan Yuli
Hajiya Hajara Aliyu, mahaifiyar jarumi a Kannywood Alhassan Kwalle, ta rasu a gidan ta da ke unguwar Bachirawar Madugu, a Ƙaramar Hukumar Ungogo a cikin garin Kano.
Lahadi, 13 Ga Watan Agusta
Allah ya ɗauki ran jaruma a Kannywood, Malam Hauwa Magaji Gwarzo, a gidan ta da ke unguwar Kakuri Hausa, Kaduna.
Lahadi, 20 Ga Watan Agusta
Allah ya yi wa tsohuwar jarumar Kannywood, Hannatu Umar Sani, rasuwa, ta rasu a gidan yayar ta da ke unguwar Katampe, Abuja.
Laraba, 23 Ga Watan Agusta
Allah ya ɗauki ran furodusa a Kannywood Aminu S. Sufi. Aminu ya rasu a gidan sa da ke Titin Lokoja, unguwar Rigasa, Kaduna.
Alhamis, 31 Ga Watan Agusta
Hajiya A’isha, mahaifiyar Abba El-Mustapha ta rasu a Kano.
Laraba, 6 Ga Watan Satumba
Allah ya ɗauki ran mahaifiyar jarumi kuma mai bada sutura a Kannywood Umar Big Show. Hajiya Hauwa Hussaini ta rasu a asibitin Nassarawa da ke Kano.
Laraba, 6 Ga Watan Satumba
Allah ya yi wa mahaifin darakta a Kannywood Sadiq S. Hussaini Jepp rasuwa. Alhaji Salisu Hussaini Maigwanjo ya rasu a gidan sa da ke unguwar Fagge ‘Yantaya, Kano.
Asabar, 9 Ga Watan Satumba
Mawaƙiya Hauwar Aleebaba, ta rasu sanadiyyar banke ta da mota da wani matashi ya yi a Kano.
Talata, 12 Ga Watan Satumba
Hajiya Habiba Yusuf, mahaifiyar tsohuwar jaruma Hadiza Maina, ta rasu Asibitin Barau Dikko da ke Kaduna.
Asabar, 30 Ga Watan Satumba
Malama Sabira Ishaq Koli, matar furodusa kuma ɗan kasuwa a Kannywood Alhaji Rabi’u Koli, ta rasu a Asibitin Manal da ke Kawo, Kaduna.
Laraba, 4 Ga Watan Oktoba
Allah ya ɗauki ran jarumar Kannywood, Hajiya Binta Ola. Hajiya Binta ta rasu a gidan ta da ke Sabuwar Unguwa cikin birnin Katsina.
Asabar, 14 Ga Watan Oktoba
Malama Fatima Muhammad, mahaifiyar furodusa a Kannywood Hamisu Bawasa, ta rasu a gidan ta da ke ‘Yantukwane, Tudun Wada, Kaduna.
Alhamis, 19 Ga Oktoba & Asabar, 28 Ga Oktoba
Allah ya ɗauki ran mahaifiya da yayan jarumin Kannywood, Tanimu Akawu. Hajiya Amina ta rasu a gidan ‘yar ta da ke Layin Zana a cikin garin Jos, Jihar Filato. Shi kuma Alhaji Mustapha ya rasu a hanyar kai shi asibiti kafin rasuwar mahaifiyar su, tsakanin su kwana tara.
Asabar 11 Ga Watan Nuwamba
Allah ya ɗauki ran shahararren ɗan wasan kwaikwayo, Alhaji Usman Baba Pategi (Samanja) a Asibitin Garden City da ke Titin Sultan cikin garin Kaduna.
Asabar, 18 Ga Watan Nuwamba
Alhaji Ibrahim Sa’idu Gamagira, mijin furodusa kuma tsohuwar shugabar Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), reshen Jihar Kaduna, ya rasu Belam Hospital da ke Abuja.
Litinin, 20 Ga Watan Nuwamba
Allah ya ɗauki ran darakta a Kannywood Aminu S. Bono. Ya rasu a gidan sa da ke Kano.
Talata, 12 Ga Watan Disamba
Allah ya ɗauki ran jarumi Auwal Bauchin-Bauchi. Ya rasu a wani asibitin kuɗi da ke hanyar Jos a garin Bauchi.