Kannywood

Ummi Rahab Ta Bayyana Cewa Zata Tona Ma Adam Zango Asiri

Matashiyar Jarumar KannyWood Ummi Rahab (Ummi) Ta Bayyana Cewa Idan Har Kaci Gaba Da Batamin Suna (Adam A Zango) To Saina Tona Maka Asiri.

Inda Jarumar Ta Wallafa Bayanin A Shafinta Na Instagram Bayan Da Adam A Zango Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Ya Raba Gari Da Jarumar A Cikin Shirinshi Na (Farin Wata Series)

Adam A Zango Wato Ubangidanta Ya Shaida Cewa Yarinyar Yana Neman Daurata A Kan Hanyar Tarbiyya Ne Sai Kuma Yaga Kullun Tana Kara Bigirewa Hakan Ne Yasa Su Raba Gari Da Ita.

Ga Cikakken Videon Da Adam A Zango Yayi Bayani Akan Rabuwarsu Da Ita Jarumar

Sai Dai Ita Jarumar Ta Musanta Haka, Inda Tace Idan Har Yaci Gaba Da Neman Bata Mata Suna. Ita Kuma Zata Tona Mishi Asiri, (Duniya Tasan Halin Da Ake Ciki Tsakaninsu Da Ita)

Ummi rahab adam a zango

Sai Dai Tana Wallafa Wannan Bayanin Jim Kadan Ta Gogeshi A Shafinta Na Instagram Din.

Kuci Gaba Da Bibiyarmu Domin Ci Gaba Da Samun Cikakken Labarin.

Back to top button
error: Content is protected !!