Labarai
Umarni A Bamu Daga Sama Kan Mu Saki Murja
Sakon Takarda Aka Turo Mana Daga Kotu Domin Mu Saki Murja Kunya Amma Ba Guguwa Tayi A Hannunmu Ba Inji Kakakin Gidan Yarin Da’ Daure Murja IbrahimKunya
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa Kakakin gidan gyaran hali na jihar Kano AC Misbahu Kofar Nassarawa ya shaidawa DAILY NIGERIAN cewa sananniyar ‘yar Tiktok Murja Kunya ba guduwa ta yi daga gidan yari ba.
A cewar sa, tun ranar Alhamis takarda ta zo daga kotu don neman a sake ta, kuma gidan yarin ya sake ta a ranar.
Ya ƙara da cewa kotu ce ta kawo ta ajiya a wajensu, kuma kotu ce ta ce su sake ta.*