KannywoodUngategored

Tsun-tsun soyayyata ya koma kan Lukuman –Rayya

Tsun-tsun soyayyata ya koma kan Lukuman –RayyaJarumar fina-finan hausar nan Surayya Aminu wadda akafi sani da Rayya ta bayyana cewa a yanzu tsun-tsun soyayyarta ya tashi daga kan Yakubu Kafi Gwamna, da Yawale ya koma kan dan gidan gwamna mai ci wato Lukuman.

Rayya ta bayyana hakan ne ya yin da take zantawa da Dala FM a safiyar litinin da ta gabata, ta ce a yanzu Kafi Gwamna yana gidan gyaran hali, don haka ya barar da soyayyarsa, shi kuwa Yawale dama son maso wani yake.Biyo bayan cigaban wasan kwaikwayon nan mai nisan zango na “Kwana Casa’in” da tashar Arewa 24 ke hasakakawa ya nuna yadda sabuwar soyayya ta fara kulluwa tsakanin jaruma Rayya ‘yar aikin gidan tsohon gwamna Bawa Mai Kada da kuma dan gwamna mai ci Malam Adamu wato Lukuman.

Idan zaku iya tunawa dai a kwanakin baya ne jaruma Rayya ta karyata rade-radin da ake yadawa na cewa sun fara soyayya ta zahiri da abokin aikinta wato Yawale.

Back to top button
error: Content is protected !!