Kannywood

Tsohuwar Jarumar KannyWood Farida Jalal Ta Yi Aure Na 3 A Asirce

Tsohuwar Jarumar KannyWood Farida Jalal Ta Yi Aure Na 3 A Asirce

Mawakiyar Yabon Annabi (S.A.W) Kuma Tsohuwar Jaruma A Masana’antar KannyWood Wato Farida Jalal Ta Sake Aure Na Uku, A Asirce A Garin Katsina.

AN ɗaura auren tsohuwar jarumar Kannywood kuma mawaƙiyar bege, Sayyada Farida Jalal, tare da mawaƙin yabo Shariff Ibrahim Gombe Ranar Juma’a a Data Gabata A Garin Katsina..

Shaidun gani da ido sun bayyana wa mujallar Fim cewa Babban Limamin Masallacin Juma’a na Katsina, Liman Malam Ɗayyabu Ratibi, shi ne ya ɗaura auren a kan sadaki N100,000.

Da ta ke yi wa mujallar Fim ƙarin bayani game da wannan aure nata wanda kuma shi ne na uku, Farida Jalal ta ce auren kawai aka ɗaura a Katsina amma daga baya za a yi shagalin bikin a Kano.

Ta ci gaba da cewa mijin nata shi ma sha’iri ne saboda haka mawaƙiya ta auri mawaƙi kuma duk na yabon Ma’aiki SAW.

Ta ce: “Mun haɗu da wannan mijin nawa a Kano sakamakon waƙoƙin yabo da mu ke yi tare. Kuma zan ci gaba da yin waƙoƙi na kamar yadda na saba yi bisa amincewar miji na.”

Haka kuma tsohuwar jarumar ta ce ita kaɗai ce a gidan mijin nata, saboda haka za ta sakata ta wala.

Ta ƙara da cewa insha-Allah wannan aure mutu ka raba ne, takalmin kaza.

Wannan aure dai an yi shi ne ba tare da gayyatar ‘yan fim na Kano ko na Katsina ba, sai dai Farida ta faɗa wa mujallar Fim cewa za a yi gayya idan an fitar da lokacin da za a yi shagalin bikin a garin Kano.

Allah Ya Basu Zaman Lfy.

Source- Fimmagazine.com

Back to top button
error: Content is protected !!