Kannywood

Tsofaffin Jaruman Kannywood Mata (15) Da Suka Dawo Fim Bayan Mutuwar Auren Su

Kamar yadda muka ruwaito muku a rahoton dawowar jaruma Farida Jalal harkar fim, cewa yanzu kamar yayi ne ake na dawowar tsofaffin matan da suka taka rawa a masana’antar Kannywood, hakan yasa muka bincika muka zakulo muku wasu daga cikin jaruman Kannywood mata da suka taka rawar gani a baya a masana’antar ta Kannywood kana kuma bayan mutuwar auren su suka dawo harkar.

Koda yake wasu bamu da tabbacin sun dawo fim din ka’in da na’in kasancewar bamu gansu cikin fim ba amma akan gansu jefi-jefi cikin ‘yan fim din, amma kuma da yawan su sun tabbatar da dawowar su inda wasu suka bayyana da bakin su wasu kuma kawai sai ganin su aka cigaba da yi a cikin fim.

Ga dai jerin jaruman a kasa:

1. Hadiza Kabara

2. Hafsat Shehu

3. Fati Muhammad

4. Maijidda Abbas

5. Fati Baffa Fage

6. Farida Jalal

7. Rukayya Dawaiya

8. Saima Muhammad

9. Samira Ahmad

10. Fauziyya Mai Kyau

11. Sadiya Gyale

12. Sadiya Kabala

13. Maryam Ab Yola

14. Tumba Gwaska

15. Fati KK

Maryam Ab Yola, Sadiya Kabala da Tumba Gwaska ba za a kira su da tsofaffin jarumai ba kasancewar ba wacce ta shekara goma a masana’antar a cikin su sai dai sun shiga wannan lissafi ne saboda sun yi aure kuma sun fito sun cigaba da harkar.

Haka zalika ba wai ana nufin wadannan sune kawai jaruman Kannywood mata da su kai aure suka fito ba amma sune ake kyautata zaton sun dawo harkar fim, kuma ana ganin su ne a cikin dukkan sha’ani na ‘yan fim.

Back to top button
error: Content is protected !!