Labarai

Tsakanin Sheikh Zakzaky Da Wasu Jaridun Arewa: Wanene Maƙaryaci?

Tsakanin Sheikh Zakzaky Da Wasu Jaridun Arewa: Wanene Maƙaryaci? Daga Comrade Yahaya M Abdullahi: Barkanmu da shan ruwa a wata mai alfarma ƴan Uwana musulmi, kwanaki biyu Alƙaluman wasu cikin jaridu da kuma wasu da ke kiran kansu marubuta sun yi rubdugu akan Jagoran Harkar Musulunci Sheikh Ibraheem Zakzaky akan maganan da yayi na Harbin da Sojojin Najeriya suka masa a Zaria ranar 12 ga watan Disambar 2015 a Idonsa, wanda har cewa yayi Idonsa ya fita.

Na zata ganin labarin zai sa wasu mutane su tausaya wa wannan Dattijon da ba wanda ya taɓa jinsa yayi ƙarya koda a wasa ne ballanta a zahiri, amma sai ya zamanto aka mayar da lamarinsa Izgili da kuma wasa da Dariya, wasu ma murna suke (Allah ya sawwaƙe), to don Allah yaushe ne Arewa zamu zama Mutanen da zamu ga wani namu a cikin wani hali mu tausaya masa?

Sheikh Zakzaky: Mutum ne da ba wanda a faɗin Duniyar nan zai ce maka ya taɓa masa ƙarya ko kuma ya Faɗi maganan da ba dai-dai ba, shine yayi magana akan Zamfara da wasu jihohin arewa na abubuwan da zasu faru tun kafin su faru, in muna da matsala da Aƙidar da Shaikh Zakzaky yake kai kada mu rufe Ido kuma akan ƴancinsa, mu ajiye Aƙidanci a gefe mu yi magana a matsayin Mutane masu Mutunci in muna da Mutuncin kenan, shi Mutum ne kuma Malami mai jama’a da yawa don Allah wani riba zaka ji in ka zage shi ko ka masa Izgili?

Ɗalibin kiwon lafiya dake Karatu a Ƙasar China Najib Umar Maigatari yayi ƙarin bayani akan wannan mummunan cuta wanda saboda Harbin da akayi wa Malamin ya kamu da wannan cutar, dukkan likitoci sunyi bayyana yana ɗauke da wannan cutar saboda Harbin da Sojojin suka masa a gidansa, yaya wannan Cutar take?

GLOBE LUXATION (Popped Out Eye).

Abun da Malam bahaushe ke kira kwayar ido (eyeball), ba wai a rike yake gam a cikin kurmin ido (eye socket) ba kamar yanda mutane da yawa ke tunani.

Akwai tsokoki (muscles), jijiyoyi da kuma wasu sauran ‘connective tissues’ da su ka rike kwayar idon, su ke ba shi damar juyawa daidai bukata (in all directions): sama da kasa, gefe da gefe, da sauran su. Shi kurmin ido (eye socket) wanda ya ke kasusuwa (bones) ne mabanbanta su ka hadu su ka samar da shi, babban amfanin sa shi ne bayar da kariya ga kwayar ido (eyeball) da kuma sauran ‘apparatus’ na gani (vision).

A likitance, fitowa/zazzadowar kwayar ido (eyeball) daga cikin kurmin ido (eye socket) zuwa waje sanannen abu ne. Ana kiran shi da ‘globe avulsion/luxation’ (fincikewar/zazzadowar kwayar ido daga cikin kurmin da ke ba shi kariya).

Sannan kuma, ficewar kwayar idon ma hawa-hawa ne: akwai wanda kwayar ido zai saki (yana cikin kurmin ido, amma ya cire daga wani bangare na shi)- wannan bai da tsanani sosai (mild to moderate); akwai kuma mai tsanani (severe) wanda baki daya kwayar idon za ta fice daga cikin kurmin ido ta fito waje. Daga cikin su, na karshe (wanda kwayar ido zai fito baki daya) ne ba a cika samu sosai ba, har ma an rubuta takardun nazari da bincike (research papers) akan wasu ‘cases’ na faruwar shi da su ka zo da abun mamaki (ba zan kawo nan ba, amma akalla mutum na iya bincikawa ya gani).

Sannan yanayin fitowar ma ya bambanta, idan kwayar ido ta fice baki daya, za ta iya bulluqowa waje kai tsaye (anteriorly), ko ta yi ciki wajen saitin hanci (nasally), ko kuma ta yi wajen kunci (temporally). Ko kuma ta yi wani wajen da ya hada sauran (of course akwai effect din gravity da zai ja shi zuwa kasa ko a wane direction ya fito, tunda yana reto ne a jikin wani abu da ya rike shi daga ciki).

Jin ciwo (trauma) shi ne babban abun da ke kawo ficewar kwayar ido (traumatic globe luxation) wannan zai iya zama buguwar ido, dukan ido, cakewar ido, harbi da sauran su. Baya ga jin ciwo, akwai sauran cututtuka kamar ciwon dajin bayan kwayar ido (retrobulbar tumor), cututtukan rashin karfin ‘connective tissues’ kamar su Ehlers Danlos Syndrome, da sauran su; duk su na iya sanya kwayar idon mutum ya zazzado waje idan abu ya yi tsanani.

Kuma idan ya faru, ana mayarwa ne a hade shi da abun da ya yi saura, bayan wani lokaci mutum zai dawo ya ci gaba da gani da idanun. Sai dai kuma idan a garin ficewar wani abu mai muhimmanci- misali jijiyar gani (optic nerve) ta samu matsala, ko wani abu makamancin haka; wannan ganin mutum ba zai dawo yanda ya kamata ba.

To ban san me mutane ke yiwa izgili dangane da maganar Sheikh Zakzaky na cewa an harbe shi, kwayar idon shi ta fita ta yi wajen kunci ya dawo da ita ba! Abu ne sananne, ya na nan a rubuce a litattafai, maqalu, kai har ma da takardun bincike da nazari na fannin likitancin ido. Ko me ya kawo karyatawa da izgili kuma? Jahilci, qiyayya, hassada, ta’assubanci ko kuma duka?

Nayi tunanin a halin da muke ciki a Arewacin Najeriya baza mu taɓa kyamar wani Mutum koda ba musulmi bane daga Arewa ballantana Musulmi kawai bambancin Aƙidace a tsakani, a halin da muke ciki a yanzu fa wasu yankunan bama ta addini akeyi ba ko aƙida, ta rayuwa ake yi, wanda yake wasu daga cikin yankunan Zamfara, Kaduna, Katsina, Niger, Sokoto zai shaida maganata, to amma Meyasa mu da ya kamata mu taya su da wasu abubuwa tun daga addu’a da sauransu sai ya zamanto Izgili wa Malamanmu ya zama Aikinmu?

Domin yanke uzuri ga masu neman gaskiya, hoton da ke kasa sakamakon ‘CT Scan’ ne da aka yiwa Shaikh Zakzaky wanda ya nuna guragutsan harsashi (bullet fragments) makale a cikin kashin kurmin kwayar idon Malamin wanda ya ke tabbatar da gaske an harbe shi ba sau daya ba a idanun shi. Aqalla idan mutum na da Ra’ayin karyata mutane, don ya na ganin abun da su ka fada kamar wani ‘subjective evidence’ ne, aƙalla mutum ba zai iya karyata hoton da ke kasa ba ko? Tunda shi ‘empirical evidence’ ne. Abun da ya rage kuma, mutum ya je bincika shin harbin bindiga zai iya cire kwayar ido baki daya ko ba zai iya cirewa ba?!

A ƙarshe ina kira ga ƴan Uwana Ƴan Arewa don Allah muyi Ɗabi’u na gari da soyayya ga junanmu ba tare da duba Aƙidaci ba.

Comrade Yahaya M Abdullahi, Ɗan Jarida kuma Marubuci.

Back to top button
error: Content is protected !!