Labarai

TINUBU Ya Nada Ɗan Gidan Ganduje Mukami

Shugaban Kasa Bola Ahmad TINUBU Ya Nada Ɗan Gidan Ganduje Mukami A Hukumar Samar Da Wutar Lantarki A Karkara

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da shugabannin gudanarwa na hukumar samar da wutar lantarki a karkara bisa zargin almundaha tare da maye gurbinsu da wasu ciki har da Umar Abdullahi Umar, ɗa ga mai girma tsohon gwamnan Jihar Kano, kana kuma shugaban riƙo na jam’iyyar APC ta ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito, waɗanda shugaban ƙasar ya dakatar ɗin sun haɗa da:

1. Alaniyi Alaba Netufo, a matsayin babban daraktan hulɗa.

2. Barka Sajou, a matsayin babbar darakta kan harkokin gudanar da ayyuka

3. Sa’adatu Balgore, a matsayin babbar darakta kan harkokin kuɗaɗen gudanarwar hukumar.

Baya da haka, shugaban ƙasar ya buƙaci a zurfafa bincike a kansu dangane da tuhumar da ake musu ta kashe sama da Naira Biliyan 1.2 ba bisa ƙa’ida ba shekaru biyu baya. Wanda kuma tuni hukumar yaƙi da cin-hanci da rashawa ta samu nasarar gano wasu daga cikin kuɗaɗen.

Nan take kuma, shugaban Tinubu ya umarci a maye gurbin waɗanda aka dakatar ɗin da wasu ƴan ƙasa waɗanda suka cancanta a matsayin riƙon ƙwarya. Waɗanda aka naɗa ɗin sun haɗa da:

1. Abba Abubakar Aliyu, a matsayin shugaba.

2 Ayoade Gboyega, a matsayin babban daraktan hulɗa.

3. Umar Abba Umar, a matsayin daraktan ayyuka.

4. Doris Uboh, daraktan kuɗaɗe na hukumar.

5. Alufemi Akinyelure, shugaban kulawa da gudanuwar ayyuka.

Shugaba Tinubu ya hore su da su gudanar da ayyukansu daidai da ƙudiri da tanadin doka.

Back to top button
error: Content is protected !!