Labarai

Tinubu Ya Bada Umarnin Bai Wa Ƙananan ‘Yan Kasuwa Tallafin ₦150,000 a Jigawa

Tinubu Ya Bada Umarnin Bai Wa Ƙananan ‘Yan Kasuwa Tallafin ₦150,000 a Jigawa

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin bada tallafin Naira 150,000 ga kowane dan kasuwa a jihar Jigawa.

Sanarwar hakan ta fito ne daga fadar shugaban kasa ta hannun mataimakinsa Kashim Shettima wanda ya rabawa manema labarai a Jiya Talata a birnin Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

Kashim Shettima ya bayyana cewa, Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin bayar da tallafin Naira 150,000 ga kowane mai kasuwanci a jihar Jigawa, kuma tallafin wani bangare ne na tallafin da Gwamnatin Tarayya ke bayarwa ga ƙananan ‘yan kasuwa fadin kasar.

Ya ce tallafin ₦150,000, kyauta ne, don haka waɗanda suka amfana ba za su biya ba.

Back to top button
error: Content is protected !!