Kannywood
Tausayina Yakamata Aji Ba Tsangwama Ba – Inji Rahama Sadau
Rahama Sadau ta bayyana cewa a duk wannan abin da ya faru kamata yayi aji tausayina ba Tsangwamata Ba.
Ta bayyana hakane a hirar da ta yi da BBChausa kan Hotunan da ta dora a shafinta na Twitter da riga me budadden baya wanda suka jawo cece-kuce har akawa Annabi(SAW) batanci.
Rahama ta bayyana cewa, ta saka hotunan a shafinta na Twitter da dare inda ta kwanta, tace da Safe data farka sai ta ga comments wajan Dubu 10, tace wanine ya aika mata da batancin da wancan yayi wanda kuma dalilin haka yasa ta cire hoton.
Rahama da take martani kan abinda abokan aikinta ke cewa kan Lamarin, tace kamata yayi a tausaya mata, kamata yayi a yi tunanin shin ita a wane irin hali take ciki ya take ji kan wannan lamarin?