Kannywood

Tashin Hankali Biyar Da Baza A Manta Dasu Ba har Abada A Kannywood

Abubuwa da dama sun faru tun bayan kafuwar masana’antar fina-finai ta Kannywood fiye da shekaru ashirin da suka gabata .

Sai dai akwai fitattun abubuwa da suka fi janyo kace-nace musamman a ‘yan shekarun baya-bayan nan Mun yi nazari akan abubuwa guda biyar da suka fi tayar da kura a masana’antar wacce ke da farin jini sosai.

1. Abu na farko shine maganar auren jinsi Abinda ya ja hankali sosai kuma ya tada jijiyar wuya shine maganar hada auren jinsi da aka yiwa wasu taurarin Kannywood hudu da yin dabi’ar a watan Afrilun shekarar 2007, lamarin da ya saka suka shiga wasan buya da hukumar Hisba, bayan ta samu labarin sannan ta shiga nemansu.

Ko da yake a wata hira da ta yi da jaridar BBC, Aunty Maiduguri wacce aka zarga da hada auren ta musanta zargin.

2. Sai kuma abu na biyuwato gagarumar matsala da ita ma baza a manta da ita ba a wannan masana’antar ta Kannywood wato maganar fina-finan batsa.

‘Yan Kannywood sun samu kansu a tsaka mai wuya a watan Agustan shekarar 2007, inda aka zargi Maryam Usman Hiyana da saurayinta Usman Bobo da yin fim din batsa.

Fim din da aka yi ta yadawa kuma ya janyo matukar suka ga masu harkar fina-finan, wanda daga nan jarumar da abin ya faru da ita tayi sallama da masana’antar inda taje tayi aurenta, yanzu haka kuma tana gidan mijinta tare da ‘ya’yanta.

3. Daga nan kuma sai matsala ta uku wadda ita ma ba za a manta da ita ba, wato maganar zargin neman maza.

A cikin wani watan Agusta ne kuma zargin neman maza ya dabaibaye masana’antar lamarin da ya kai har fitaccen jarumin nan kuma mawaki, Adam A Zango rantsuwa da alkur’ani mai tsarki yana kare kansa.

Batun ya taso ne bayan da aka zargi wasu daga cikin masu harkar fim din cewa ‘yan luwadi ne. Sai dai a wannan karon babu wani mutum daya da aka fayyace sunansa.

4. Sai kuma abu na hudu da aka sha maganganu akwai wanda gaba daya Malaman addini sai dai suka shigo maganar, wato maganar gina alkaryar fim wanda ake kira da (Fim Village) wanda gwamnatin tarayyar Najeriya tayi kokarin ginawa a lokacin.

Batun gina alkaryar fim a jihar Kano wanda gwamnatin tarayyar ta so gabatarwa ya tayar da jijiyoyin wuya a baya a watan Yulin bana. Malaman addini da jama’a ne suka nuna adawa da shirin, suna masu cewa zai daurewa badala da shashanci gindi a jihar.

Malaman sun zargi ‘yan fim din da cewa mutane marasa kamala dake yada batsa. Sai dai masu shirya shirya fim din sun ce ba haka lamarin yake ba, kuma mummunar fahimta ake yi musu.

5. Sai kuma abu na biyar kuma na karshe daga cikin abubuwan da muka binciko na abubuwa marasa dadi da suka faru da masana’antar ta Kannywood da baza a taba mantawa dasu ba har abada.

Abu na biyar din shine maganar jaruma Rahama Sadau wadda ta rungume wani mawakin gambara na Hausa wato Classiq a wani fai-fan bidiyo da suka fito.

Batun rungumar mawakin nan Classiq da Rahama Sadau ta yi shi ne abu na baya-bayan nan da ya ja hankalin masu bin al’amuran Kannywood da ma jama’ar gari. Yayin da wasu ke sukarta kuma kungiyar shirya fina-finan Hausa ta kore ta, Rahama ta nemi gafara tare da kokarin fahimtar da mutane cewa duk abin da ta yi a wakar aikinta ne ya bukaci haka ba son rai ba.

Daga Jaridar Legit

Back to top button
error: Content is protected !!