Taron Yi Wa Ƙasa Addu’a Muka Je Fadar Shugaban Ƙasa Ba Maulidi Ba – Alaramma Ahmad Suleiman
Taron Yi Wa Ƙasa Addu’a Muka Je Fadar Shugaban Ƙasa Ba Maulidi Ba – Alaramma Ahmad Suleiman
Sanannen mahaddaccin Al- Ƙur’ani na kungiyar Izala Alaramma Ahmad Suleiman, ya bayyana cewar gayyatar da Uwargidan Shugaban kasa A’isha Buhari ta yi wa Malamai zuwa fadar shugaban kasa, gayyata ne akan yi wa ƙasa addu’a da kuma cigaban ƙasa, amma ko kaɗan gayyatar ba ta da alaƙa da taron maulidi kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka rinƙa yayatawa.
Alaramma Suleiman ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu ta wayar tarho dangane da ziyarar da malamai suka kai fadar shugaban kasa a yau.
Babban Alaramman ya cigaba da cewar, Uwargidan Shugaban kasa Aisha Buhari ta gayyaci dukkanin malamai daga kowane ɓangare na addinin musulunci Izala da ɗarika, kuma an buƙaci malaman da gudanar da Addu’oi tare da tambihi akan wasu abubuwa da suka shafi ƙasa, malamai irin su Sheikh Muhammad Bin Usman da Sheikh Saleh Pakistan da sauran su da dama duk sun gabatar da jawabai, lokacin da Malam Ibrahim ɗan gidan Sheikh Ɗahiru Bauchi ya tashi yin jawabi shine ya shigo da maganar maulidi inda yake cewa gashi a yanzu muna cikin watan maulidi da ya kamata a martaba shi.
Nan take Sheikh Abdallah Pakistan ya mike ya yi jawabin cewa ka da a kauce daga ainihin abin da ya tara mu anan, mun zo gabatar da addu’a ga ƙasa ne ba taron maulidi ba, amma abin mamaki sai ga wasu kafafen yada labarai sun ɗauki labari mara tushe ballantana asali na cewar wai malaman Izala sun je taron maulidi.
Alaramma Ahmad Suleiman ya shawarci kafafen yada labarai da su rinƙa tantance gaskiyar labari kafin yaɗawa mutane, sannan ya buƙaci jama’a da su rinƙa gudanar da bincike a duk lokacin da wani sabon labari ya zo garesu domin kaucewa shiga ruɗani.