Tana Yunƙurin Barin Musulunci Saboda Damuwa!
Duk Wanda Ta Nemi Taimako Wajensa Kan Tsananin Rayuwar Da Ta Ke CIKI, Sai Ya Nemi Kwanciya Da Ita Kafin Ya Taimake Ta, Don Haka Take Tunanin Fita DAGA Musulunci A Matsayin Mafita Gareta!

Ga Zazzafar Martani Daga – Ahmad Nagudu
To, yanzu ban da batan basira ba, tsakanin aikata zunubi ki na matsayin musulma da fita daga Musuluncin gaba daya, wanne ne ya fi a irin rashin lissafin na ki?
Kin ce duk wadanda ki ke neman taimakon a wajen su, sai sun bukaci kwanciya da ke tukunna. To, yanzu a wajen ki, da aikata z! na gwara fita daga Musuluncin ko?
Dan tsaya! Amma dai dama can ba Musulma ba ce, shigowa ki ka yi, shiyasa yanzu ki ke neman hanyar fita saboda Allahn da aka ce ki yi imani da shi bai yi miki yadda ki ke so ba ko?
Idan kin fita da musuluncin wane Addinin za ki koma? Tsakanin musulunci da sauran Addinan, wanne ya fi tsanantawa kan haramta Zinar?
Duk halin da ki ke ciki, kin kai mutanen Zirin Gaza ne? Kin san me ya ke faruwa a can kuwa? Akwai wadanda duk wayewar garin duniya sai sun fita sun yi Bara su ke iya ciyar da kan su. Ya ya ki ke da su?
Wai dan dakata, a wane gari ko yanki ko jiha ki ke rayuwa ne ma wai tukunna?







