SubhanaAllah! Wannan Fim Din Kwata Kwata Baikamata Ace Ayishi Ba. Domin Babu Wani Ilmantarwa Saidai Barna Mai Yawa A Ciki,
An Saki Tallan Wani Fim Wanda Mata Ke Koyar Da Yanda Ake Jima’a A Hausa, Fim Din Mai Suna (Makaranta) Inda A Fim Din Banda Rashin Kunya Da Nuna Lalata Ba Abin Da Akeyi.
Bai Kamata Hukumar Tace Fina Finai Ta Bari A Saki Wannan Fim Din Ba, Saboda Gujewa Abin Da Zai Je Ya Dawo.
Kalli Tallan Fim Din Anan.
Rabiu
Agaskiya wannan film din babu tunani a cikinta, shi film idan za’ayi akan yi la’akarine da yanayin al ummar da film din ya shafa, ba mamaki anyi wannan film din ne da nufin gyara amman irin wannan gyaran barna ce Don haka yakamata hukumar tantance fina finan Hausa su kula sosai wajen tantance film kafin saketa. ALLAH sa mudace.
A gaskiya akara tunani akan wannan film dinndan bakaramar illa zai haifarba musammam ga yayanmu musulmai(hausawa) kuma kusa in cewa duk wadda talalace sanadiyyar wannan film din to kuma kuna da kamasho aciki.
Dama yaya lafiyar kura bare tayi hauka don Allah ayi hakuri da yinsa domin ba zai amfanar da komai ba sai karin tsunduma ma al, umma a wani fasadin
Dan allah Dan annabi karku saki wannan film dinnan sabida mahassadanmu zasu samu galaba akanmu idon kunsaki wannan film karkumanta hakan zai iya jawo sanadiyar rufe kamfaninnaku idon ana Sara anaduba bakin gatari Allah ya Kare nagaba
A gsky wanan Bai kamata ba
Gaskiya wannnan fim din baizo daidai da koyarwar addinin mu da al’adar muba
Dan haka kamata ma yayi ahukunta masu fim din
In har aka saki wannan flim din ko itace zatai silar ruguje war kannywood gabaki daya
Lallai wannan film din cin mutuncin addinin musulunci neh da al’adar hausa domin hk dukwanda yake da iko kuma yabari aka sake wannan film wallahi munbarshi ga Allah bamu yafemasa bah kuma muna rokon Allah daya la’anci masana’antar Fina finan don ikonahi da isansho
A tallan ma baku tsira ba. Insha Allahu karshenku yazo
Subhanallah 🙆 abin har ya Kai ga haka? To uban giji Allah yayi Mana tsari da shaidanun mutane
Mahukuntan Kannywood aiki ya sameki domin kuwa bahaushe Yana cewa “Wake Daya shike Bata Gari” Allah ya tsaremu da tsarewarsa
Inna lillahi wa,inna ilaihin raji,in
A gaskiya wannan ba firm bane andai bullo da wata hanya ta gurbata tarbiyyar yaran mu
A gaskiya wani sabon bala,I zaku bullo mana da shi Dan Allah a sake tunani
Sannan mahukunta kuna gani wannan sam bai kamata ba saboda ya sabawa addini da kuma al,adarmu Dan Allah a duba
Hakikanin gaskiya wannan film din, saidai kawai ya lalata rarbiyya