Kannywood

Tabbas Afakallahu na kokari wajen tsaftace Kannywood –Kamaye

Fitaccen jarumin fina-finan hausar nan kuma marubuci mai shirya fina-finai Dan’azimi Baba wanda akafi sani da kamaye, ya bayyana cewa yanzu haka masana’antar Kannywood ta kama hanyar gyaruwa sakamakon kokarin hukumar tace fina-finai ta jihar Kano.

Yayin wata tattaunawa da jarumin yayi da Freedom Radio ya bayyana cewa a yanzu masana’antar Kannywood ta dauko hanyar gyaruwa bisa kokarin da shugaban hukumar tace fina-finai da daba’I ta jihar Kano Alhaji Isma’il Na’abba Afakallah ke yi.
Kamaye ya kara da cewa yana goyon bayan yunkurin tsaftace fina-finan hausa dari bisa dari da Afakallahun ke yi a Kano.

Idan zaku iya tunawa a kwanakin baya ne dai wata dambarwa ta kunno kai tsakanin wasu jaruman masana’antar da suke zargin ana musu rashin adalci, a yayin ayyukan hukumar tace fina-finan ta jihar Kano.

Wannan dambarwar dai ta haifar da ficewar wasu jarumai daga masana’antar baki daya.

Back to top button
error: Content is protected !!